
Daga Umar Garba a Katsina
Rundunar ƴan sandan jihar Katsina ta ce jami’anta sun yi nasarar daƙile wani harin ƴan bindiga waɗanda suka yi yunƙurin garkuwa da wasu matafiya a hanyar Magama zuwa Katsina.
Manhaja ta samu labarin cewa, da yammacin jiya Lahadi ƴan ta’adda da kawo yanzu ba a san su ba ɗauke da bindigu ƙirar AK-47 sun tare hanyar inda suka far wa wata mota ƙirar J5 tare da yin garkuwa da fasinjojin dake ciki mutum bakwai daga bisani kuma suka bankawa motar wuta.
Kakakin rundunar ƴan sandan jihar, ASP Abubakar Sadiq ya tabbatar da faruwar lamarin cikin wata sanarwa da ya fitar jiya Lahadi.
“A ranar 17 ga watan Agusta, 2024, da misalin qarfe 12 na rana, ɓarayin daji ɗauke da muggan makamai irin su AK-47, sun tare gadar Kukar Babangida da ke kan titin Magama zuwa Katsina, inda suka kai hari kan wata mota ƙirar J5., sun yi garkuwa da mutane bakwai tare da ƙone motar.
“Samun labarin ke da wuya, DPO na ƙaramar hukumar Jibia, ya haɗa tawagar ƴan sanda tare da haɗin gwiwar jami’an tsaron al’umma da ƴan banga inda suka fatattaki ɓarayin.”
Kakakin ya ci gaba da cewa, “Rundunar ta mayar da martani inda bayan musayar wuta inda jami’an tsaron suka samu nasarar ceto mutanen da ɓarayin suka yi yunqurin shiga daji da su.
“Rundunar ta yi nasarar daƙile yunƙurin sace mutanen tare da kuɓutar da su.
“Sai dai ɗaya daga cikin waɗanda lamarin ya rutsa da su ya samu rauni a kafadarsa sakamakon harbin ƴan bindigar, inda nan take aka garzaya da shi asibiti don samun kulawar likita.”
A cewar sanarwar yanzu haka ana bi sawun ƴan bindigar don cigaba da daƙile mummunar aniyarsu ta yin garkuwa da mutane.
