Daga MAHDI M. MUHAMMAD
Mataimakin Shugaban ƙasa, Kashim Shettima, ya yi watsi da iƙirarin cewa, gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na yin sakaci da Arewacin Nijeriya, yana mai jaddada cewa, bai kamata a riƙa alaƙanta yankin da talauci ba, idan aka yi la’akari da ɗimbin albarkatunta.
A wata hira da Rediyo Faransa (RFI) Hausa, a ranar Lahadi, Shettima ya kare matakin da gwamnati ta ɗauka, inda ya bayyana cewa Arewa ce fifiko ga harkokin gwamnatin Tinubu.
Da yake magana a kan zanga-zangar da aka yi a baya-bayan nan, ya ce, “Muna cikin tsarin dimokuraɗiyya, kuma kowane ɗan ƙasa na da ‘yancin faɗin albarkacin bakin sa cikin lumana. Duk da haka, dole ne mu kiyaye da ’yan siyasa masu mugun nufi ko ’yan iska da za su iya tada hargitsi. Abin da ya faru kwanan nan ya kasance abin takaici da damuwa ga al’umma da gwamnati.”
Dangane da ƙalubalen da yankin Arewa ke fuskanta, Shettima ya jaddada cewa gwamnati ta duƙufa wajen magance su.
“Gwamnati na da kyakkyawar niyya ta taimaka wa mutanenmu a Arewa,” inji shi.
“Mun ware naira biliyan 100 domin tallafa wa harkar noma, da nufin taimakawa manoma miliyan 500, waɗanda akasarinsu ‘yan Arewa ne. Bugu da ƙari, shugaban ƙasa ya kafa ma’aikatar kiwo don tallafa wa yankin, kuma mun saki tan 42,000 na abinci don rage tsadar rayuwa.”
Shettima ya kuma bayyana ƙarin mafi ƙarancin albashi daga N30,000 zuwa N70,000 a wani ɓangare na ƙoƙarin gwamnati na rage wahalhalu.
“Mun san mutanenmu suna shan wahala, kuma mun ƙuduri aniyar yin duk mai yiwuwa don taimaka musu,” inji shi.
