Ƙungiyar ƙwadago ta shiga taron gaggawa kan zargin ta’addanci

Spread the love

Shugabannin ƙungiyar ƙwadago sun shiga wani taron gaggawa tare da shugaban su Joe Ajaero a hedikwatar su da ke Abuja.

Taron ya biyo bayan wata gayyata da hukamar ‘yan sanda ta yi wa Shugaban ƙungiyar bisa zargin cewa ya na taimakawa ‘yan ta’adda da laifukan yanar gizo.

Takardar mai kwanan wata 19 ga watan Agusta ta samu sa hannun ACP Adamu Mu’azu a madadin kwaminshinan ‘yan sanda.

Takardar ta buƙaci Joe Ajaero ya kai kansa hukumar domin amsa tambayoyi, rashin yin hakan ya zama karya doka wanda hukumar ba za ta ɗauka da wasa ba.

By ukarofi