NLC ta yi barazanar shiga yajin aiki matuƙar aka cutar da shugabanta

Spread the love

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI

Ƙungiyar ƙwadago ta Ƙasa, NLC ta umarci mambobinta a faɗin Najeriya su fara yajin aiki daga tsakiyar daren yau matuƙar aka cutar da shugabanta, Joe Ajaero da wasu manyan jami’ainta.

Hakan na zuwa ne bayan da rundunar ƴan sanda ta gayyace shi ofishinta kan zargin sa da hannu acikin ɗaukar nauyin ta’addanci, sata ta yanar gizo da zamba cikin aminci.

Cikin wani saƙo da ƙungiyar ta fitar bayan kammala wani zaman gaggawa da Majalisar Zartarwa, FEC, hukumar ta yi watsi da tuhume-tuhumen da ke kan shugaban nata, ta na mai cewa hakan tasirin siyasa ne da ke ƙoƙarin ƙasƙantar da matsayinsa.

A wata takarda da ke ɗauke da sanya hannun Mataimakin shugaban NLC, Ado Sani Minjibir, ƙungiyar ta ce ta girmama gayyatar da rundunar ƴan sandan ta yi wa Ajaero, sai dai ta na buƙatar ƙarin lokaci saboda yanayin zargin da ake masa.

By Babaji