NNPC ta tabbatar da biyan kuɗi amma ba na tallafi ba

Spread the love

Hukumar NNPCL ta musanta zargin da ake mata na biyan kuɗin tallafi, ta bayyana cewa ba wanda ta biya tallafi wata tara da ya shuɗe.

Babban jami’in kamfanin da ke kula da harkokin kuɗi Umar Ajiya ya bayyana haka a Abuja ranar Litinin.

Ya bayyana cewa kamfanin na kula da bambacin farashi wajen shigo da mai ƙasar. Kamfanin bai biya kuɗin tallafi ga kowanne mutum ba tsawon wata takwas da ya wuce. Kuɗin da kamfanin ke biya kuɗin bambancin farashi ne wajen shigo da man amma ba tallafi ba ne.

Ya bayyana cewa, bambancin kuɗin farashi ne suke magana kuma wannan tsakanin kamfanin ne da gwamnatin tarayya ba da wani ɗan kasuwa ba.

By ukarofi