Hukumar Kula da Cututtuka masu yaɗuwa ta Najeriya (NCDC) ta sanar a ranar Juma’a cewa ƙasar ta samu mutane 40 da aka tabbatar suna da ƙyandar biri daga cikin mutane 830 da ake zargin suna da cutar.
Darakta-Janar na NCDC, Dokta Jide Idris, ya sanar da hakan a taron haɗin gwiwa na NCDC/WHO na ƙasa game da ƙyandar biri tare da masu ruwa da tsaki a Abuja.
WHO a Najeriya ta bayyana cewa Najeriya za ta samu alluran rigakafin ƙyandar biri kyauta daga Gwamnatin Amurka.
Idris ya bayyana, “A halin yanzu, muna da mutane 40 da aka tabbatar suna da cutar daga cikin mutane 830 da ake zargin suna da cutar. Ba mu samu wani mutum ya mutu ba. Mun kafa tsarin aiki na gaggawa don magance cutar ta hanyar amfani da ginshiƙai daban-daban.
“Mun haɗu da gwamnatocin jihohi da kwamishinonin kiwon lafiya na jihohi don ba su shawara kan kafa shirin gaggawa da tsarin aiki.
“Wani muhimmin yanki shi ne kulawa. Daga cikin mutane 40 da aka ba da rahoto a ƙasar, sun rabu a cikin jihohi kusan 12 ko 13. Mutane da yawa suna cikin Kudancin kasar, tare da wasu a Legas, Ogun, da sauran yankunan arewa. Tsarinmu shine mu yi amfani da waɗannan jihohi don rage yawan mutane da ke da cutar da kuma gudanar da sanya idanu don gano ƙarin mutane.”
Shugaban NCDC ya kuma lura cewa hukumar tana buƙatar “ƙara inganta ɗakunan gwaje-gwaje. An tabbatar da dukkan mutane da aka tabbatar da yanzu ta amfani da genomic sequencing a cikin dakunan gwaje-gwaje biyu – National Refrence Lab a Abuja da Legas. Saboda yaduwar cutar, muna buƙatar ƙara yawan dakunan gwaje-gwaje.
Idris ya bayyana cewa akwai buƙatar ƙara samun ɗakunan gwaje-gwaje musamman a yankunan kudancin ƙasar, ya ƙara da cewa cibiyar tana ƙara ƙoƙarin wayar da kan jama’a game da cutar, alamunta, da matakan hana yaɗuwarta.
