NGO ta koya wa mata 100 sana’o’i a Gombe

Spread the love

Daga ABUBAKAR A BOLARI. Gombe

A ƙoƙarin ta na ganin ta rage talauci ta yaƙi zaman banza a jihar Gombe, musamman a tsakanin mata, gidauniyar Motherhen Deɓelopment Foundation ta koyawa Matan karkara guda 100 sana’o’i daban-daban don su samu hanyar dogaro da kai.

Da ta ke jawabi a wajen yaye matan da suka shafe watanni uku zuwa huɗu suna koyan sana’ar a garuruwan Shongo Idrisa Lafiya Mango da Abuja Bula a yankin ƙaramar hukumar Akko Kwamishinar Ma’aikatar Mata da Walwalar su Asma’u Iganus, ta ja hankalin matan da cewa kar su ga sun yi abun sayarwa ba a saya ba su karaya haka kasuwa ta ke idan yau ba a sa yaba gobe za a saya.

Asma’u Iganus wacce Daraktar tsare-tsare ta ma’aikatar Bathsheba Samuel ta wakilta ta ce abinda ma’aikaar mata ya kamata ta yi ne ba su yi ba gidauniyar Motherhen take yi amma da yake suna da kyakkyawar dangantaka shi ya sa suke goya musu baya.

Ita ma shugabar hukumar tattara haraji na jihar Hajiya Aisha Adamu, cewa ta yi wannan aniya ta gidauniyar Motherhen abun a yaba musu ne domin sun ceto matan karkara daga zaman banza sun koya musu sana’o’in da za su dogara da kan su har ma su taimaki wasu

A jawabinsa Lamido Gona Alhaji Umar Abdulkadir Abdussalam shi ma yabawa Mother hen din ya yi da cewa yaji dadi na yadda wannan gidauniya ta fara koyawa mata sana’a a yankin sa

Lamido Gona wanda Sakataren Majalisar sa Abdulra’uf Mohammad Bello, ya wakilta yace da za a samu wasu kungiyoyi kamar Mother hen da mata da yawa basa zaman banza a Gombe

A nata shugabar gidauniyar Dokta Erisa Sarki Danladi, cewa tayi sun hada kai ne da Deɓelopment Eɗchange Centre wato DEC wajen koyawa mata sana’o’in da suma suka bada injinan niƙa da ake nika dawa da shinkafar da ake yin gari da shi

Dokta Erisa, ta ce sun zakulo matan ne sun koma musu yadda ake sarrafa garin Dawa dan yin kunu da kuma yadda ake busar da tattasai da Attaruhu da ma Albasa da kuma yadda ake hada man girke mai hade da Borkono da yajin daddawa da kantu da sauran abubuwa daban.

Ta kuma yi kira da cewa a dinga sayen kayan da aka sarrafa din a wajen su domin kara musu kwarin guiwar ci gaba da yin sana’ar.

A garin Abuja Bula, ma irin taron aka gudanar inda nan ma aka samu jawabai masu kama hankali da jan kunne da aka dinga yi wa matan kan su riƙe sana’ar da aka koya musu hannu bibiyu.

ƙungiyar matar na Abuja Bula, mai suna Alheri Abuja Bula Kiyari, bayyana jin daɗinsu suka yi matuƙa kan wannan shiri na gidauniyar Mother hen Deɓelopment Foundation.

By ukarofi