Yaƙi da cin hanci da rashawa na buƙatar taron-dangi, inji Shugaba Tinubu 

Spread the love

Daga USMAN KAROFI 

Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya yi kira ga ƙasashen ƙungiyar ECOWAS da su amince da kuma aiwatar da daftarin yarjejeniyar yaƙi da cin hanci da rashawa. 

A yayin da yake jawabi a taron shekara-shekara karo na 6 Na ƙungiyar Taron Dangin Yaƙi Da Cin Hanci da Rashawa Ta Yammacin Afirka (NACIWA) a Abuja, shugaba Tinubu ya jaddada buƙatar ɗaukar ƙwararan matakai da zaƙewa a yayin yaƙi da cin hanci da rashawa dake addabar yankin.

Shugaban wanda mataimakinsa Kashim Shettima ya wakilta ya sanar da bayar da gudummawar ginin ofishin dindindin ga hedikwatar ƙungiyar ta NACIWA, kana ya buƙaci ƙasashe mambobin ƙungiyar da su bari a ga yaƙin a aikace maimakon a takarda, sannan su mai da hankali kan bin ƙa’idojin shara’a da inganta haɗin gwiwar ƙasa da ƙasa, tare da baza gaskiya a faifai ga al’umma a yayin yin amfani da albarkatun ƙasa ko sayo kayayyakin gwamnati.

Shugaba Tinubu ya bayyana illolin cin hanci da rashawa, da cewa wata cuta ce mai karya garkuwar zamantakewa ta hanyar cin amanar jama’a, da gurgunta rarraba albarkatun ƙasa cikin adalci. 

Don haka a cewarsa, Nijeriya ta shirya tsaf don tabbatar da samun nasarar NACIWA a yankunan ECOWAS a babban shirinta na yaƙi da cin hanci da rashawa.

Taron ya samu halartar manyan baƙi da dama da suka haɗa da ministan harkokin wajen Nijeriya Ambasada Yusuf Tuggar; Babban Lauyan Tarayya kuma Ministan Shari’a, Lateef Fagbemi; da Shugaban Hukumar Yaƙi da yi wa Tattalin Arziki Tu’annati (EFCC), Mista Ola Olukoyede.

By ukarofi