Kisan Sarkin Gobir: Ƙalubalenmu ‘yan Arewa

Spread the love

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU

Ina rubutun nan a yayin da idanuna ke cike da ƙwalla, zuciyata a ƙuntace, sakamakon labarin kisan gillar da ‘yan bindiga suka yi wa Sarkin Gobir Alhaji Isa Muhammad Bawa bayan sun yi garkuwa da shi da ɗansa da wani ɗan uwansa har tsawon kwanaki 26. Babu shakka ba ni kaɗai ba, jama’a da dama daga Jihar Sakkwato da yankin Arewa bakiɗaya sun ji baƙin ciki da takaicin abin da ya faru da wannan babban basarake, wanda kafin rasuwar sa shi ne Hakimin Gatawa a ƙaramar Hukumar Sabon Birni da ke Jihar Sakkwato.

Hankalin ‘yan Nijeriya ya ƙara tashi ne tun bayan da waɗannan ‘yan ta’adda suka yi garkuwa da shi, lokacin da suka fitar da wani bidiyonsa, yana cikin wani mawuyacin hali, yayin da hannayensa da ƙafafunsa suka kasance a ɗaure, farar rigar da yake sanye da ita duk ta ɓaci cikin jini. Babu shakka ba iyalansa kaɗai ba, duk wani mai tausayi da imani a ransa sai hankalinsa ya tashi da ganin wannan bidiyo, wanda a ciki aka ji marigayin yana roƙon a ceci rayuwarsa ta hanyar biyan kuɗin fansar da waɗanda ke riƙe da shi suka nema, musamman Gwamnatin Jihar Sakkwato.

Wani bidiyo da na gani, wanda Sanata Shehu Sani daga Jihar Kaduna ya fitar shi ma ya yi matuƙar nuna damuwarsa da halin da aka nuna marigayin, yana mai ƙalubalantar manyan Arewa da su tashi tsaye su yi wani abu a kai, domin rashin kunya da rashin mutuncin da ‘yan ta’addan nan ke yi ya ta’azzara, kuma dole ne a taka musu birki. Idan ba haka ba abin ba zai yi wa Arewa da shugabanninta daɗi ba. Har ma kuma ya ja hankalin su ‘yan bindigar da cewa, su tuba su daina abin da suke yi, domin babu amfanin da hakan zai musu, ko al’ummar da suke ikirarin karewa. 

Waɗannan kalamai na Sanata Shehu Sani sun yi min daɗi, duk da kasancewar ya yi su ne a cikin wani yanayi na alhini. Amma gaskiya ce mai ɗaci ya faɗa mana. Ita kuma gaskiya kamar yadda marigayi Sa’adu Zungur ya faɗa, bata neman ado ko na zaƙin muryar zabiya. Dole ne a faɗe ta a yadda take ko ta yi daɗi ko ba ta yi ba.

Kamar yadda a baya Arewa ta yi sakaci ta naɗe hannu fitinar Boko Haram ta yi ƙamarin da ta mamaye illahirin yankin da halaka rayuka da dama, haka yanzu ma tun muna ɗaukar wannan abin kamar wasa ne, har gashi ya fara cin rayukan sarakuna da iyayen ƙasa. Wani matashi ɗan Arewa daga Jihar Gombe, Suleiman Omar Farouk, ya koka da halin da ake ciki a Arewa, inda cikin wani taƙaitaccen rubutu da ya yi ya bayyana cewa idan an yi shiru waɗannan ‘yan ta’addan suna kashe Sarki mai cikakken iko da tarihi a ƙasar nan, gobe kuma wani babban malamin addini wanda jama’a ke ganin kimarsa da darajarsa a ƙasar nan za su kashe. Kuma tabbas yana da gaskiya, domin tun abin nan na ƙarami, inda ana ji da ganin yadda suke ɗaukar talakawa marasa gata da ‘yan makaranta suna garkuwa da su ana basu kuɗin fansa, ba a dakatar da abin ba, har ta kai ga yanzu shugabannin al’umma suke ɗauka suna garkuwa da su, tare da yi musu kisan gilla a gaban iyalansu da jama’arsu. 

Rahotanni sun tabbatar da yadda waɗannan ’yan bindiga suke hallaka mutane tare da yin garkuwa da ‘yan makaranta da talakawa a jihohin Neja, Zamfara, Kaduna, Katsina da Sakkwato. Akasari mutanen da suke ɗauka suna garkuwa da su ne domin a basu kuɗin fansa su je su sayo makamai, su yi sharholiya da kuɗin. A baya suna kai hari ne kan mai-uwa-da- wabi ne don kama mata da ƙananan yara mata suna yi musu fyaɗe da wulaƙanta su, tare da kashe iyayensu maza. Amma a yanzu suna ɗaukar mutane ne na musamman a gidajensu ko wuraren ayyukansu. Kamar ’yan siyasa, malaman jami’o’i, jami’an tsaro, manyan, ’yan kasuwa, da kuma masu riƙe da rawanin sarauta. 

Wani rahoton tashar Muryar Amurka ya bayyana yadda ayyukan ’yan bindiga ya kassara cigaba a yankin arewa maso yammacin ƙasar nan, inda shi ne yanki mafi girma da ake noman kayan abinci, amma yanzu saboda satar mutane da hare-hare, manoma da dama sun ajiye garma da fatanya, saboda tsoron rayuwarsu. A wasu wurare ’yan bindigar da kansu suke ƙwace gonakin mutane, sannan su bautar da su da ƙarfin bakin bindiga su sa su nome musu gonakin. Wasu kuma sun ƙwace wuraren aikin haƙar ma’adinai sun zama su ne kaɗai suke da iko da wuraren. 

Saboda nuna isa da bunƙasa ma, waɗannan tsageran ’yan bindiga har sanyawa ’yan uwan waɗanda suka kama suke yi kan su kai musu kayan abinci ko babura masu ƙira iri kaza, da maƙudan kuɗaɗe, kafin su saki waɗanda suka kama. Kamar wani al’amari na baya-bayan nan da ya faru, a yankin Gonin Gora da ke Jihar Kaduna, inda wasu ’yan bindiga suka ɗauke wasu mutane 16, sannan daga bisani suka buƙaci a biya su Naira Tiriliyan 40 da manyan motoci ƙirar Hiluɗ guda 11 da babura da ake yi wa laƙabi da Boko Haram guda 150, kafin su saki mutanen. 

Su ma ’yan bindigar da suka sace marigayi Sarkin Gobir irin buƙatar da suka nema kenan, cewa a basu Miliyan 60 da babura ƙirar Boko Haram kafin su sako shi. Amma duk da haka kafin a kai musu kaya da kuɗaɗen da suka nema sun kashe shi. Wani ɗan uwan marigayi ya bayyana cewa, ɗan jinkirin da aka samu na kai kuɗaɗen ya faru ne sakamakon wahalar neman baburan da ake buƙata, waɗanda babu su a gari. Bayan samun labarin kisan marigayin, an dakatar da ba da kuɗin, amma su ’yan bindigar sun matsa sai an bayar da waɗannan kuɗaɗe kafin su saki gawarsa da sauran mutanen, da suka haɗa da yaronsa da ɗan uwansa. 

Wani abin takaici da baƙin ciki shi ne, wata majiya marar inganci kawo lokacin haɗa wannan rubutu, ta ce bayan miƙa musu abin da suka buƙata ‘yan bindigar sun saki mutanen amma sun hana gawar marigayin, tare da cewa sun binneta da kansu! Wannan wulaƙanci har ina? Fisabilillahi!!! 

Yanzu haka shugabannin mu na Arewa da masu ƙarfin faɗa a ji za su yi shiru wannan abin ya cigaba? Lokaci ya yi da za mu yi duk mai yiwuwa mu tabbatar da ganin ƙarshen wannan ta’addanci da tsageranci, ko a ina suke! Kuma ko su wane ne suka aikata wa wannan dattijo bawan Allah haka lallai ne a nemo su! Ba ma su kaɗai ba, dukkan ‘yan ta’addan da suke cin karensu babu babbaka a dazukan jihohin Arewa, musamman Kaduna, Katsina, Zamfara, Neja, da Sakkwato dole ne jami’an tsaro su tabbatar sun yi abin da ya dace a yi maganinsu. 

A jawabinsa na jajentawa da ta’aziyya da shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya fitar ta hannun kakakinsa Ajuri Ngelale ga iyalin marigayin da sauran ‘yan Nijeriya, ya bayyana kisan gillar da aka yi wa basaraken a matsayin babban abin tashin hankali da firgici, wanda kuma gwamnatin tarayya ba za ta zuba ido ya tafi a banza ba. Tilas ne, a cewarsa sai an shawo kan waɗannan matsalolin tsaro da suka addabi ƙasar nan. 

Ya kamata wannan abin da ya faru ya zama mana izina garemu al’ummar Arewa da Nijeriya baki ɗaya, masu mulki, ‘yan kasuwa da talakawa, lallai mu ga  an yi wa marigayi Alhaji Isa Muhammadu Bawa adalci bisa kisan gillar da aka yi masa da sauran ‘yan Nijeriya. Sannan lallai Gwamnatin Jihar Sakkwato da manyan ‘yan siyasar yankin su fito su gaya wa iyalin marigayin, jama’ar Sabon Birni da Masarautar Gobir yadda wannan abin ya kasance a kan idonsu, tun kafin su fuskanci fushin Allah da na jama’ar su. 

Allah Ka yi mana maganin wannan musiba a ƙasar nan, Ka kawo mana sassauci kan fitinar da muke fuskanta a ƙasar nan yau da gobe. 

By ukarofi