Ƙungiya ta koya wa mata 100 sana’o’i a Gombe

Spread the love

Daga ABUBAKAR A BOLARI a Gombe

A ƙoƙarin ta na ganin ta rage talauci ta yaƙi zaman banza a Jihar Gombe, musamman a tsakanin mata, Gidauniyar Motherhen Deɓelopment Foundation ta koya wa matan karkara guda 100 sana’o’i daban-daban don su samu hanyar dogaro da kai.

Da ta ke jawabi a wajen yaye matan da suka shafe watanni uku zuwa huɗu suna koyan sana’ar a garuruwan Shongo Idrisa Lafiya Mango da Abuja Bula a yankin ƙaramar Hukumar Akko, Kwamishinar Ma’aikatar Mata da Walwalar su Asma’u Iganus, ta ja hankalin matan da cewa kar su ga sun yi abun sayarwa ba a saya ba su karaya haka kasuwa ta ke idan yau ba a saya ba, gobe za a saya

Asma’u Iganus wacce Daraktar tsare-tsare ta ma’aikatar Bathsheba Samuel ta wakilta ta ce, abin da ma’aikatar Mata ya kamata ta yi ne ba su yi ba gidauniyar Motherhen take yi amma da yake suna da kyakkyawar dangantaka shi ya sa suke goya musu baya.

Itama shugabar hukumar tattara haraji na jihar, Hajiya Aisha Adamu, cewa ta yi wannan aniya ta gidauniyar Mother hen abun a yaba musu ne domin sun ceto matan karkara daga zaman banza sun koya musu sana’o’in da za su dogara da kan su har ma su taimaki wasu

A jawabin sa Lamido Gona Alhaji Umar Abdulkadir Abdussalam shi ma yaba wa Motherhen ɗin ya yi da cewa ya ji daɗi na yadda wannan gidauniya ta fara koyawa mata sana’a a yankinsa.

Lamido Gona wanda Sakataren Majalisar sa Abdulra’uf Mohammad Bello, ya wakilta yace da za a samu wasu ƙungiyoyi kamar Motherhen da mata da yawa basa zaman banza a Gombe.

A nata ɓangaren, shugabar gidauniyar Dokta Erisa Sarki Danladi, cewa ta yi sun haɗa kai ne da Deɓelopment Eɗchange Centre wato DEC wajen koyawa mata sana’o’in da suma suka bada injunan nika da ake niƙa Dawa da Shinkafar da ake yin gari da shi

Dokta Erisa, ta ce sun zaƙulo matan ne sun koma musu yadda ake sarrafa garin Dawa dan yin kunu da kuma yadda ake busar da tattasai da attarugu da ma albasa da kuma yadda ake haɗa man girke mai haɗe da borkono da yajin daddawa da kantu da sauran abubuwa da dama.

Ta kuma yi kira da cewa a riƙa sayen kayan da aka sarrafa zin a wajen su domin aara musu kwarin gwiwar ci gaba da yin sana’ar.

By ukarofi