Gwamnan Jihar Kogi, Usman Ododo ya san ya cece-kuce a shafukan yanar gizo a dalilin ganin shi da a ka yi a wata liyafar gwamnonin PDP a Jihar Taraba.
Taron liyafar wanda gwaman Jihar Adamawa ya wallafa a shafin sa na X cewa an yi wannan liyafar ne domin nunawa duniya irin al’adun da ke wannan yankin.
A wannan taron ne a ka hango gwamnan Jihar Kogi, Usman Ododo, wanda taron ya nuna cewa taron gwamnoni ne na PDP amma abun mamaki sai a ka hango shi.
Mutane sun shiga mamaki ganin cewa bai fi yan sa’o’i kaɗan da babbar kotun ƙasa ta tabbatar ma shi da kujerar shi a matsayin gwamna.
Wani a shafin X @princeofiaga ya bayyana cewa “wannan ba Ododo bane da kotu ta tabbatar mai da kujera ba, ina Tinubu yake?”
Wannan fitowar dai ta jawo cece-kuce da dama ga mutane. Amma gwamnan ya fito ya kare shi ta hanyar mai magana da yawun shi Femi Fanwo ya ce gwamna ya je taron biki ne amma ba taron PDP ba.
