
Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI
Babbar kotun tarayya da ke Abuja, ta bayar da izini ga ƴan sanda su tsare wasu masu zanga-zangar tsadar rayuwa da aka kama na tsawon kwana 60 kafin a ƙarƙare gudanar da bincike akan su.
Mai Shari’a Emeka Nwite ta bayar da izinin bayan da wani Ibrahim Mohammed a madadin Sufeton ƴan sanda ya shigar da takardar ƙararraki akan su inda za a tsare su har zuwa lokacin kammala binciken.
Cikin takardar da aka miƙa wa kotun a ranar 9 ga watan Agusta, an shigar da sunayen masu zanga-zanga guda 75 waɗanda shekarunsu ke tsakanin 14 da 34.
Matasa sune; Abubakar Ibrahim (18), Abubakar Adam (19), Suleiman Ali (16), Mubarak Mas’ud (23), Umar Musa (19), Aminu Hussaini (20), Umar Kabir (23), Ibrahim Musa (24), Abba Usman (30), Umar Inusa (18), Tasi’u Lawan (17), Ibrahim Rabi’u (16) da Jamilu Haruna (16).
Haka kuma akwai; Muktar Yahaya (17), Abdulbasit Abdulsalam (34), Salisu Adamu (16), Bilal Auwalu (15), Abdul’aziz Adam (15), Sadiq Sunusi (15), Muhammad Musa (14), Usman Amiru (14), Abdulganiyu Musa (15), Muhd Yahaya (19), and Sunusi Nura (14) da dai sauran su.
A na zargin su ne da aikata laifukan ta’addanci da cin amanar ƙasa waɗanda ƴan sandan suka ce sun saɓa wa sakin layi na 2(1) da (3) da kuma na 24 da 26 da dokar hana ta’addanci a kundin dokar ƙasa na 2022.
Elizabeth Ogochukwu ita ce Sakatariyar bincike ta sashen leƙen asiri (IRT) a hedkwatar ƴan sanda da ke Abuja, inda ta ce ofishin Sufeton ƴan sanda ta hannu ofishin mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkar tsaro, NSA ya samu rahoton sirri da ke nuna cewa an shirya tayar da tarzoma da ke adawa da gwamnatin tarayya da ta jihohi.
Ta ce, an kama matasan ne kan cewa a na zargin su da hannu acikin tada tashin-tashina a wasu sassan Nijeriya wanda hakan ya haifar da salwantar dukiyoyi da rayukan al’umma.
