Taɓargaza: Mai shayi ya sheƙe matashi saboda taliya da madara a Jigawa

Spread the love

Daga UMAR AKILU MAJERI a Dutse

Tafaru ta ƙare a wani shagon sayar da shayi inda mai shayin ya yi anfani da wani ƙaton itace ya sheƙe wani matashi saboda yana zarginsa da sace masa kayan shayi a unguwar Jigawar Tsada da ke Ƙaramar hukumar Dutse ta Jihar Jigawa

Ana zargin mai sayar da shayin ya yi ta dukan matashin da itace ne har sai da ya daina yin nunfashi saboda wai yana zargin ya sace taliyar indomi a shagonsa da yake sana,ar sayar da shayi a unguwar Jigawar Tsada ta Jihar Jigawa.

Wannan mummunan lamari ya faru ne a jiya Litinin Kamar yadda bayanai suka nuna. Kuma ance wai dama ya jima yana zargin sa da satar kayan shayi a shagon, lamarin da yasa ya yi ta fakonsa har zuwa wannan rana da ajali ya yi Kiran matashin mai kimanin shekaru 20 a duniya.

Mai shayin ya zargi mamacin da satar taliyar yara wato indomi da burodi da madara da kuma man fetur a shagon sa, lamarin da ya kai ga sa-in-sa a tsakaninsu kafin mutuwar sa

Ana cikin haka ne mai shayin, a fusace ya ɗaure saurayin da igiya, ya yi ta bugunsa har sai da ya ga ya daina motsi.

Daga bisani ’yan sanda suka je suka ƙwace shi suka garzaya zuwa asibitin koyarwa na Rasheed Shekoni, amma da zuwansu aka tabbatar ma su da mutuwarsa.

Jawabin hakan ya biyo bayan sanarwar faruwar lamarin da kakakin rundunar ’yan sanda da Jihar Jigawa, DSP Lawan Shiisu Adam, ya sanyawa hannu a ranar Talata. Wanda ake zargin ya amince da aikata laifin kisan kai tare da ɗaukar doka a hannu inda ya bayyana cewa yawan satar da mamacin ke masa ce ta fusata shi ya aikata laifin kisan Kan

.A cewarsa, wanda ake zargin ya shaida wa masu bincike cewa a baya ya sanar da iyayen mamacin, amma babu wani mataki da aka ɗauka.

Jami’in ‘yan sanda ya ce, maƙwabta sun ce sun ji kukan mamacin yana neman agaji amma sun kasa shiga tsakani har sai da ’yan sanda suka iso.

Kakakin Rundunar ‘yan sanda ya ce bayan cikakken bincike za su gurfanar da wanda ake zargi da kisan a gaban kotu domin ya fuskanci hukunci.

By ukarofi