
Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI
Hukumar kula da gudanar Kuɗaɗen Ƙasa, FRC tayi nasarar tilasta hukumomi da wasu ofisoshin gwamnati tarayya dawo maƙudan kuɗaɗe da adadinsu ya kai Naira tiriliyan biyu zuwa asusun kuɗin shiga (CRF) tun daga shekarar 2007.
Shugaban hukumar, Barista Victor Muruako ya faɗi hakan a Abuja a lokacin da reshen hukumar na jihar Bauchi ya kai ziyarar nazari na kwana ɗaya inda ya bayyana irin rawar da FRC ke takawa wajen tabbatar da gaskiya da adalci a ofisoshin gwamnati.
Ya ce, hukumar ta na aiki tuƙuru wajen kula da kuma nazari kan kasafin gwamnatin tarayya ga rassanta guda uku gami da nazari kan asusun gwamnati.
Ya ƙara da cewa, hukumar ta bada taimakon kayan aiki ga gwamnatocin jihohi wanda hakan ya taimaka wajen samar da rassan hukumar a sama da jihohi 15 a Nijeriya.
Kazalika, dokar hukumar ta umarci hukumomin gwamnati su ke mayar da kaso 80 na rarar da ake samu a yayin gudanar da ayyukansu.
Bugu da ƙari, hukumar ke da alhakin kula da nazarin harkokin kuɗi da kuma ƙarfafa tsarin gudanar da ƙuɗaɗe ga hukumomi.
