Gwamnatin Zamfara ta canza ranakun koma wa makaranta

Spread the love

A ƙoƙarin ta na daidaita zangon karatu na jihar Zamfara da na sauran jihohi, gwamnatin jihar Zamfara ta ɗage ranar komawa makaranta a zangon karatu na 2024/25.

A wata sanarwa da ma’aikatar ilmin jihar ta fitar, ta bayyana cewa ta mayar da ranar komawa makaranta zuwa ɗaya ga watan Satumba 2024. Sanarwar ta bayyana wannan a matsayin wani tsari domin daidaita tsarin karatun jihar da na sauran jihohi baki ɗaya don shiga tsarin ƙasa baki ɗaya.

Daga ƙarshe gwamnatin ta yi kira da iyaye da malaman makaranta su bada haɗin kai domin ganin wannan tsari ya daidaita komai.

By ukarofi