’Yan fansho sun buƙaci Tinubu ya dakatar da tsarin PenCom

Spread the love

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Ƙungiyar ’yan Fansho ta Nijeriya, COPRAN, ta ce, tsarin Hukumar PenCom ya na ƙara tsananta ƙalubalen rayuwa ga su ‘yan fansho a ƙasar.

COPRAN, a wata takardar koke ga shugaban ƙasa Bola Tinubu, shugaban majalisar dattawa, kakakin majalisar wakilai, ministan kwadago, da hukumar kare haƙƙin bil’adama, da dai sauransu, sun ce ’yan fansho suna sha wuya da PenCom bayan sun yi ritaya.

Shugaban ƙungiyar ta COPRAN, reshen jihar Filato, Anthony Ayiwulu, ya ce manufar PENCOM, duk da cewa an yi shi da gaskiya, ta fi cutar da ma’aikatan gwamnati da suka yi ritaya, waɗanda kuma ake kira da manyan mutane.

Ayiwulu ya ce, akwai buƙatar a sauya manufar ko kuma a sake duba ta domin amfanin jama’a da ci gaban waɗanda abin ya shafa da kuma samun sakamako mai inganci.

By ukarofi