
Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, ya yi kira wajen ƙara ƙarfafa haɗin-gwiwa tsakanin Najeriya da Ƙungiyar Tarayyar Turai domin yaƙi da matsalar ƙarancin abinci mai gina jiki da sauran ƙalubalen jin-ƙai a ƙasar.
Kashim Shettima ya furta hakan ne a yayin da yake karɓar baƙoncin tawagar jakadan EU mai barin gado, Samuela Isopi a wata ziyarar bankwana da ya kai Fadar shugaban ƙasa.
Mataimakin ya kuma yaba da irin gudunmawar da ƙungiyar ta EU ke bai wa Najeriya musamman a fannin ayyukan jin-ƙai da kasuwanci.
Shettima ya yaba da ayyukan Isopi a Najeriya, ciki har da rawar da ta taka wajen ƙarfafa hulɗar EU da Najeriya wajen samar da zaman lafiya da tsaro.
A nata ɓangaren ita ma Isopi ta yi tsokaci kan ayyukanta na shekaru uku, inda ta bayyana ci gaba da haɗin-gwiwar ta samar, sannan ta jaddada ƙudirin ƙungiyar EU na cigaba da tallafa wa Najeriya a fannin zaman lafiya da tsaro, taimakon jin-ƙai, ilimi, lafiya da bunƙasar tattalin arziki.
A ƙarshe, ta kuma bayar da tabbacin cigaba da bai wa Najeriya haɗin-kan da goyon baya.
