Gwamnatin Tarayya ta bai wa ƴan kasuwa wa’adin rage farashin kayayyaki

Spread the love

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI

A ranar Alhamis ne gwamnatin tarayya ta bai wa ƴan kasuwa da sauran masu-ruwa-da-tsaki wa’adin wata guda domin su zaftare farashin kayayyaki sakamakon lalacewar da suka yi a kasuwanni.

Ta ce zata fara amfani da umarnin tilastawa idan ba su bada haɗin-kai ba.

Mataimakin shugaban Hukumar Kula da Farashi da Kwastomomi ta Ƙasa (FCCPC), Mista Tunji Bello ya faɗi hakan a Abuja, a yayin wani taron masu-ruwa-da-tsaki kan rashin tsari ga farashin kayayyaki.

Ya nuna damuwa kan yadda farashin ababe ke tashin gwauron-zabi idan an yi la’akari da yadda ake sayar da su a wasu ƙasashen da suka ci gaba.

Ya ce, rashin ƙayyade farashi acikin ƴan kasuwa ya haifar da barazana ga tattalin arziƙin ƙasa, ya na mai cewa matuƙar aka kama waɗanda suka ƙi bayar da haɗin-kan ga umarnin, to za a hukunta su ta hanyar karɓar tara da kuma tasa ƙeyar mutum zuwa gidan yari idan an samu halin hakan.

A lokacin da ya ke magana a taron, shugaban ƙungiyar ƴan kasuwa (NANT) reshen Abuja, Mista Ifeanyi Okonkwo ya ce kuɗin da ƴan kasuwa ke biya yayin shigo da kayayyaki sun taimaka wajen hauhawar farashinsu, ya na mai roƙon hukumar ta naɗa tawagar sa-ido tare da wakilci daga ɓangaren ƙungiyar don a samu shawo kan matsalar.

By Babaji