An buƙaci iyaye su guji bai wa ƙananan yara wayar salula

Spread the love

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Ɗaya daga cikin manyan kamfanonin sadarwar wayar salula na Biritaniya ya yi gargaɗi ga iyaye, inda ya ba da shawarar a guji bai wa yara ‘yan ƙasa da shekara 11 wayoyin salula.

Wannan gargaɗin yana nuna damuwa a tsakanin iyaye game da yiwuwar haɗarin da ke tattare da amfani da wayoyin hannu ga ƙanana yara.

Shawarar ta zo ne bayan wani bincike da hukumar kula da harkokin sadarwa ta Birtaniya ta gudanar, wanda ya nuna cewa kusan kashi ɗaya bisa huɗu na yara ‘yan Birtaniya masu shekaru tsakanin biyar zuwa bakwai yanzu sun mallaki wayar salula.

Yayin da iyaye sukan bayar da dalilai na tsaro don bai wa ‘ya’yansu wayoyin salula na zamani don tabbatar da cewa za su iya tuntuɓar su yayin wata damuwa, makarantu na nuna damuwa cewa waɗannan na’urori na iya fallasa ga kallon abubwuan batsa a intanet, matsalolin zamantakewa, da abubuwan da ba su dace ba.

By ukarofi