Burina gudanar da ayyukan da ƙaramar Hukumar Nasarawa za ta yi fintinkau – Zannan Kwankwasiyya

Spread the love

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano

Zannan Kwankwasiyya, jigo a jam’iyyar NNPP a Jihar Kano a ƙaramar Hukumar Nasarawa na  samun kiraye-kirayen al’umma akan ya fito neman takarar shugaban ƙaramar hukumar.

Da yake zantawa da ‘yan jarida kan wannan kira da ake masa, Hon Yahuza Gama mataimaki na musamman ga Gwamnan Jihar Kano akan kasuwanci da masana’antu ya ce bisa duba  da irin ɗinbin gudunmawa da aka bayar har Allah ya kawo Gwamnatin Jihar Kano ƙarƙashin Abba Kabir Yusuf  ake gudanar da abubuwa da dama wajen tallafawa mutane.

Ya ce dama shi tun a baya al’umma nata kiransa akan ya fito takara, domin samun hanyar da za a faɗaɗa cigaba da taimaka musu, ganin kirayen-kiraye irin wannan sun yi yawa, sai ya tuntuɓi da shawartar jagororin Kwankwasiyya da jam’iyyar NNPP na jiha da dattawa da ake da su, suka zauna da su suka sanar da su ga irin kira da ake masa, suma  sai suka nuna sha’awarsu da goyon baya akan kira da  ake na ya tsaya takarar.

Hon. Yahuza Gama ya ce shi ne sai ya gabatarwa masu ruwa da  tsaki  takardun na cewa zai   fito takara  idan Allah ya tabbatar masa,  yana da yaƙinin zai taimaki al’umma kamar yadda ya saba, duba da ana yi ne don kyautatawa da mu’amala da jinƙai, yanzu kuma in an samu wannan  damar ya zama abu na wajibi, saboda amana ce ta al’umma aka baka ka riƙe, ka kuma   tabbatarwa duk mai haƙƙi haƙƙinsu, da yardar Allah in an samu nasara za a yi abinda ya kamata.

Ya ƙara da bayyana cewa yanzu a halin da ake ciki sun sanar da dattawan jam’iyyar NNPP da na Kwankwasiyya na ƙaramar hukumar Nasarawa cewa zai tsaya neman takara kuma sun yi fatan alkhairi  da ƙarfafa masa gwiwa  saboda  irin abubuwa da suka ga yana. yi a baya da yanzu a muƙamin da Gwamna ya ba shi na mataimaki na musamman a kan harkokin kasuwanci da masana’antu sun taimaki mutane da abubuwa da dama.

Don haka ya amsa zai shiga jerin waɗanda ke neman wannan takara ta neman tsayawa  shugaban ƙaramar hukumar Nasarawa kuma yana sa ran samun nasara da yardar Allah.

Zannan Kwankwasiyya, Hon. Yahuza Gama ya yi kira ga al’ummar Nasarawa da cewa shi dama duk abinda ya gaya musu suna da yaƙinin zai kamanta, kuma za a yi abinda ya kamata in aka kai ga gaci, don haka sai su ɗage da taya shi da addu’o’i da bashi ƙarfin gwiwa da goyon baya domin su gabatar da yaƙin neman zaɓe lafiya su kai ga nasara  su yi wa mutane abubuwa da za su yi musu da gyara ƙaramar hukumar.

Ya ce idan Allah ya ba shi nasara ƙaramar hukumar Nasarawa sai ta zama abin misali a  tsakanin dukkan kananan hukumomi da ke fadin kasar nan ba ma kawai a Jihar Kano ba.

Zannan Kwankwasiyya, Hon. Yahuza Gama ya ce al’ummar Jihar Kano suna da  wayewa a harkar siyasar ƙasar nan domin  idan da ba a Jihar  Kano ba ne, samun yanldda ma za ka karɓi Gwamnati daga gwamnatin da take da Gwamnatin Jiha da ta tarayya da ta ƙananan hukumomi, amma kazo ka karɓi gwamnati idan banda al’umma da suka baiwa tsarin kwankwasiyya haɗin kai da goyon baya da hakan ma ba zata kasance ba.

Ya ce duk irin ƙulle-ƙulle da yan hamayya suke wa gwamnatin Jihar Kano ta Injiniya Abba Kabir Yusuf a yanzu abinda tasa a gaba shi take aiwatarwa, don haka ba abinda ya tsaya  na aikace-aikace duk da ƙoƙarin da maƙiya Kano suke domin ganin yadda za su daƙile Gwamnatin ko hanata aiwatar da abinda take. Gwamna Abba Kabir  Yusuf abinda ke gabansa kawai aiki za a cigaba da  ayyuka  da kyautata jin daɗin jama’a  har a gama  wa’adi a sake zaɓe kwankwasiyya  ta sake yin nasara da yardar Allah. 

Ya kafa misali da cewa a baya su ‘yan hamayya lokacin da suke a gwamnati shekara huɗu aka yi suna yi, da suka zo Abba ya kayar da su a PDP a zaɓen 2019 amma suka hana aka bar su shekara takwas suka yi ba wanda yake zuwa y a ce kaza ko a yi ƙage-ƙage a kansu, an barsu sun gama mulki aka jira lokacin da aka zo jefa ƙuri’a Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi nasara ga shi yana aiwatar da ayyukansa ta kowane ɓangare.

Hon. Yahuza Gama Zannan Kwankwasiyya ya ce a matsayinsa na mataimakin gwamna akan kasuwanci da masana’antu, ya cika umurnin jam’iyya ya ajiye muƙaminsa domin yin takarar shugaban ƙaramar hukumar Nasarawa.

By ukarofi