Daga MAHDI M. MUHAMMAD
Rundunar ’yan sandan jihar Neja ta ce ta gano wasu tarin abubuwa masu fashewa da suka haɗa da bama-bamai da na’urori masu fashewa da aka binne a wurare da dama a jihar.
Duk da cewa ana ci gaba da gudanar da bincike don gano inda bama-baman suka samo asali, amma ana zargin ‘yan ta’addan d suka addabi ƙananan hukumomin jihar ne suka ɓoye su.
Wasu daga cikin aananan hukumomin da aka gano waɗannan na’urori sun haɗa da Galadima-Kogo a aaramar hukumar Shiroro, Mutun-Daya a ƙaramar hukumar Munya, da kuma yankin Gbeganu a Minna.
Kakakin rundunar ’yan sandan, Wasiu Abiodun, wanda ya fitar da sanarwa game da lamarin a ranar Talata, ya ce sakamakon binciken na daga cikin ayyukan yaƙi da ‘yan ta’adda da aka gudanar daga shekarar 2021 zuwa 2023 da kuma ƙoƙarin haɗin gwiwa da ya shafi ’yan sanda da sauran hukumomin tsaro a jihar.
Abiodun ya bayyana cewa an kawar da bama-baman ne a ranar 22 ga watan Agusta, 2024, a wani wuri da ke bayan dutsen Zuma a Suleja, ƙarƙashin kulawar SP Mohammed Mamun, jami’in kula da EOD-CBRN (Tsarin Kashe Bama-bamai).
Sanarwar ta ci gaba da cewa, “A ci gaba da ƙoƙarin da rundunar ’, yan sandan jihar Neja ke yi na tabbatar da tsaro a jihar, kwamishinan ‘yan sandan CP Shawulu Danmamman, ya bayar da umarnin lalata wasu bama-bamai da aka gano daga wurare daban-daban, yayin gudanar da ayyukan yaƙi da ta’addanci da dama tare da sauran hukumomin tsaro a jihar tsakanin shekarar 2021 zuwa 2023.
“Kayan sun haɗa da; – IED guda huɗu da aka binne a ƙasa an gano su a Galadima-Kogo, ƙaramar hukumar Shiroro a ranar 27 ga Satumba 2021 – An ɓoye wasu bama-bamai a cikin ciyayi da kuma silindar gas mai nauyin kilogiram 5 a Mutun-Daya, aaramar hukumar Shiroro a ranar 11 ga Fabrairu 2022 – Bama-bamai sun ɓoye a cikin wani jarka mai lita goma. An gano wasu a unguwar Gbeganu da ke Minna a ranar 24 ga Oktoba, 2023.
“An samu nasarar lalata ta ne a ranar 22 ga watan Agustan 2024 a wani wuri bayan dutsen Zuma, Suleja ƙarƙashin jagorancin jami’in da ke kula da Tsarin Kashe Bama-bamai na rundunar, SP Mohammed Mamun .”
Abiodun ya ci gaba da cewa, wannan ci gaban ya zo ne mako guda bayan wasu da ake zargin ’yan bindiga ne suka kai wani mummunan hari, inda suka kashe manoma aƙalla 13 a jihar.
Idan za a iya tunawa, Galadima-Kogo a ƙaramar hukumar Shiroro ta kasance wurin da wani bala’in fashewar bam ya tashi a shekarar 2022, wanda ya yi sanadin mutuwar jami’an tsaron farin kaya da na Ciɓil Defence na Nijeriya.
