Hukumomin sufurin jiragen ruwa sun amince da mafi ƙarancin albashi kan N200,000

Spread the love

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Hukumomin jigilar kayayyaki da ke ƙarƙashin Hukumar Kula Harkokin Jiragen Ruwa, da ƙungiyar Ma’aikatan Sufurin Jiragen Ruwa ta Nijeriya (SACFEA) sun amince da sabon mafi aarancin albashi na N200,000 ga ma’aikatansu, wanda ke nuna wani gagarumin cigaba a dangantakar ƙwadago a ɓangaren ruwa.

An cimma yarjejeniyar ce bayan shafe shekaru sama da ashirin ana tattaunawar neman mafi ƙarancin albashin na ma’aikatan.

Adadin ya kai kusan kashi 54 cikin 100 fiye da yadda gwamnatin tarayya ta amince da mafi ƙarancin albashi na N70,000 a baya-bayan nan.

Idan dai za a iya tunawa, a watan Yulin 2024 ne shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya yi tayin mafi ƙarancin albashi na ga ma’aikata daga N62,000 zuwa N70,000, tare da tabbatar da cewa za a sake duba shi bayan shekaru uku, maimakon shekaru biyar. 

Sai dai a wata gagarumar nasara da aka samu, ƙungiyar SACFEA da ƙungiyar ma’aikatan ruwa ta Nijeriya (MWUN) sun sanya hannu kan yarjejeniyar a hukumance a ƙarshen mako a birnin Legas ƙarƙashin kulawar ministan harkokin ruwa da tattalin arzikin ƙasa, Adegboyega Oyetola.

Da yake yiwa manema labarai jawabi bayan rattaba hannu kan yarjejeniyar, shugaban ƙungiyar MWUN, Kwamared Adewale Adeyanju, ya ce mafi ƙarancin albashin ma’aikatan ruwa a yanzu ya kai N200,000.

Adeyanju ya ce yarjejeniyar babbar nassarace ga ma’aikatan da ke aiki tare da alawus-alawus domin samun walwalar su tare da inganta rayuwar ma’aikatan.

By ukarofi