Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Gwamnan Jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya umarci Ofishin Akanta-Janar na jihar da ya rufe duk asusun hukumomi da ma’aikatun gwamnatin jihar nan da mako guda.
Abba ya bayar da umarnin ne a lokacin da yake ganawa da Shugaban Hukumar tara Kuɗaɗen Shiga (KIRS) da kuma shugabannin hukumomi da ma’aikatun jihar.
Da yake ba da umarnin a zaman da ke gudana a Gidan Gwamnati, Abba ya ce daukar matakin ya zama dole, domin hana a karkatar da kudaden shigan jihar daga aljihun gwamnati.
Hakan kuma zai ba da damar aiwatar da tsarin asusu guda na tara kuɗaɗen shiga domin hana zurarewarsu da kuma tabbatar da shugabanci nagari.
Gwamnan ya umarci ɗaukacin shugabannin hukumomi da ma’aikatun jihar da su gaggauta bin umarnin haɗe asusun kuɗaɗen shigan a wuri guda.
“Akanta-Janar zai ba wa bankuna umarnin rufe duk wani asusun hukuma ko ma’aikatar wannan jihar, su tura kuɗaɗen da ke ciki zuwa asusun Ofishin Akanta-Janar.
“Bankunan za su ba mu takardar shaidar bin wannan umarni ta hannun Akanta-Janar da Shugaban KIRS domin ɗaukar mataki na gaba,” in ji gwamnan.
Ya ba wa al’ummar jihar tabbacin gudanar da kuɗaɗen jihar wajen bunƙasa tattalin arzikin jihar da inganta rayuwarsu da kuma a fannin ilimi, lafiya, noma da dai sauransu.
