Gwamnoni kama-karya kawai suke yi a zaɓen ƙananan hukumomi – Abba Sule Namatazu 

Spread the love

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano

Mataimakin Shugaban  Jam’iyyar PRP na ƙasa, shugaban jam’iyyar na Arewa maso Yamma  Injiniya Abba Sule Namatazu ya bayyana cewa ba wani abu a tsarin zaɓen ƙananan hukumomi  da gwamnoni na jihohin ƙasar nan ke yi sai kama-karya.

Ya ce irin wannan abu da su ke ƙoƙarin yi ba wani abu ba ne face kasuwantar da dimokwaraɗiyya da kuma killace wa kansu da ‘yan korensu kujerun mulki a matakin ƙananan hukumomi ta yadda za su cigaba da sace-sacen kayan jama’a saɓanin hukuncin kotun ƙoli da ta tabbatar da cin gashin-kai ga ƙananan hukumomin Nijeriya.

Injiniya Abba Sule Namatazu ya ce wannan mataki sun  ɗorawa duk mai sha’awar bautawa mazaɓarsa kuɗi fansa daga N10m zuwa N5m a matsayin mai takarar shugaba a ƙaramar hukumar da kansiloli duk da cewa tun daga Tinubu har Abba Kabir Yusuf ba wanda ya biya hukumar zaɓe ta ƙasa ko sisin kobo domin tsayawa takara.

Ya ƙara da cewa yin haka zai ba su damar hana sauran jam’iyyu da kuma yan jam’iyyar su ta NNPP shiga takara matuƙar ba wani ne ko gwamnati ce ta tsayar da su ba. Ya kuma  kore talakawa daga neman kujerun iko a Nijeriya komai ingancinsu.

Injiniya Abba Sule Namatazu ya ce hakan wata mumunar aƙida ce ta tabbatar da kama-karya, da ya zama dole al’umma mu tashi tsaye su yaƙe ta.

A matsayinsu na jamiyyar siyasa ta PRP, ba za su zuba ido su bar wasu tsiraru su cigaba da bautar da al’umma ba. Za su ƙalubanci wannan abu da ya kira da  “sakarci” a kotu idan har gwamnoni ba su janye maganar ɗorawa ‘yan takara kuɗin fansa ba.

By ukarofi