
Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI
Hukumomin haraji na ƙasar Jamus sun kimtsa yadda yarjejeniya tsakanin Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Nijeriya, NFF da koci Bruno Labbadia ta samu cikas.
A karon farko dai NFF ta ƙulla yarjejeniya da kocin inda daga bisani aka samu tseko kan batun haraji da hukumomin ƙasarsa suka bijiro da shi wanda ba a tsara da shi ba a baya.
Sakamakon haka ne Daraktan harkokin gudanarwa na hukumar NFF, koci Augustine Eguavoen zai karɓi ragamar jagorantar Super Eagles.
Wannan ya nuna Eguavoen shi ne kocin ƙungiyar a wasannin neman gurbin shiga gasar kofin Afrika ta 2025 da Super Eagles za ta yi inda za ta fafata da ƙasashen Jamhuriyar Benin da Ruwanda a ranakun 7 da 10 na watan Satumba da ke tafe.
Wannan shi ne karo na huɗu da Eguavoen ke jagorantar Super Eagles inda a baya ya zama mai horar da ita a 2005-2007, 2010 da kuma 2022.
