
Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Shugaban kamfanin sadarwa na optimal Image Media Limited, Dahiru Hassan ya faɗi haka a Katsina wajan buɗe taron ƙarawa juna sani da aka shirya wa jami’an yaɗa labarai na kananan hukumomi da wakilin shafukan sadarwa.
Ya ce, idan har gwamnatin ta kafa doka akan shafukan sadarwa a ƙasar, hakan zai kawo giɓi tsakani gwamnati da al’umma.
Haka kuma dokar za ta sanya gwamnati ta rinƙa musguna wa wakilan sadarwa domin ba kowane lokaci gwamnati ke da buƙatar yaɗa wasu labarai da suka shafi wasu sassan gwamnati ba.
Ya ce, dalilin shirya taron bitar shine bada horo akan sabon hanyoyin sadarwa da ya kamata su koya wajen gudanar da ayyukansu.
Ya jawo hankalin su da su yi amfani da abin da suka koya wajen taron bitar domin faɗakar da al’ummar jihar manufofin gwamnati da ƙaƙarin da take wajan inganta rayuwar jama’a.
Shugaban kamfanin sadarwar ya ƙara da cewa, dole ne jami’an yaɗa labaran da su tabbatar sun ƙara ilmantar da al’ummar jihar akan ƙoƙarin da gwamnatin jihar ke yi wajen magance matsalar tsaro a jihar.
Taron na kwana biyu jami’an yaɗa labarai na ƙananan hukumomi guda 33 da na shafukan sadarwa guda 67 su ka samu damar halarta.
Ma’aikatar yaɗa labarai ta jihar da haɗin gwiwa da kamfanin sadarwa na Optimal Image Media Limited suka shirya taron horaswa a Katsina.
