‘Yan sanda sun sake gayyatar Shugaban NLC da Sakataren ƙungiyar

Spread the love

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI

Rundunar ƴan sandan Nijeriya ta sake aika saƙon gayyata ga Shugaban ƙwadago (NLC), Joe Ajaero tare da Sakataren ƙungiyar, Emmanuel Ugboaja a wannan karon.

Saƙon na ɗauke kwanan wata kamar haka; 28 ga watan Agusta, 2024, kwana ɗaya kafin ya amsa gayyatar farko zuwa hedikwatar rundunar.

Takardar, wadda Mataimakin Sufeton ƴan sanda reshen leƙen asiri, CP Rufus Alajide ya sanya wa hannu ta ce sabon gayyatar ta samu ne don cigaba da gudanar da bincike akan zargin da aka yi masa na hannu acikin laifukan ta’addanci da damejin dukiyar ƙasa da kuma ayyukan da ka iya zama barazana ga zaman lafiyar al’umma.

A ranar Alhamis da ta gabata ne, Ajaero tare da lauyan kare ƴancin Ɗan-adam, Femi Falana da wasu mutanensa suka raka shi zuwa ofishin ƴan sandan kan gayyatar farko.

By Babaji