
Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI
Wani ɗan-kasuwa a garin Ushafa na ƙaramar hukumar Buwari da ke Abuja ya rasa ransa a lokacin da wasu ƴan ta’adda suka kai hari gidansa a ranar Alhamis.
Rahotanni sun bayyana cewa, ƴan ta’addan sun yi nasarar yin garkuwa da matarsa da ƴaƴansa a yayin farmakin.
Jami’ar hulɗa da jama’a ta rundunar ƴan sandan Abuja, SP Josephine Edeh ta tabbatar da aukuwar lamarin inda ta ce su na gudanar da bincike a kai wajen ceto matar da ƴaƴan mamacin.
Garin Ushafa wani yanki ne da ƴan bindiga ke kai hare-hare a ƴan kwanakin nan.
