
Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI
Ƙungiyar ƴan jarida reshen Abuja, tayi alhinin rashin wani babban ɗan jarida, Mista John Oba wanda ya rasa ransa bayan wata gajeruwar rashin lafiya da ya yi fama da ita.
Wata takarda da ƙungiyar ta fitar, tace Oba ɗan jarida ne da yayi aiki da gidajen Leadership da Blueprint a lokuta mabanbanta cikin jajircewa da bajinta da ya nuna a harkar aikin jarida.
Da dama daga cikin ƴan jarida sun koka game da rashin nasa inda ya kasance abin koyi a gare su.
Ƙungiyar ta ce mamaci ya kasance mai ƙoƙari sosai inda ya taka rawar gani musamman a fagensa na ruwaito labaran harkar gona.
Ta kuma aika da saƙon ta’aziyyarta ga ahalin mamacin tare fatan su kasance masu juriya a lokacin babban rashin da aka yi mu su.
