
Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI
Ƴan zanga-zangar tsadar rayuwa da aka tsare sun ƙalubalanci hukuncin da kotu ta bayar na kama su tare da tsare su yayin da suka ce gwamnatin tarayya ba ta da ƴancin yi mu su hakan.
Cikin ƙarar da masu zanga-zangar suka shigar, an samu batun da ke ƙalubalantar hukuncin da kotu ta yi a ranar 22 ga watan Agusta ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a, Emeka Nwite wanda ya umarci Sufeton ƴan sanda ya tsare su na kwana 60 har zuwa lokacin kammala bincike akan su.
Mutum 49 ne suka shigar da ƙarar a ranar 26 ga watan Agusta wadda aka sanya sunan Sufeton ƴan sanda a matsayin wanda aka kai ƙara inda lauyoyi ƙarƙashin shugabancin lauyan kare ƴancin Ɗan-adam, Femi Falana suka tsaya a kai.
A kwanakin baya ne matasan Nijeriya suka gudanar da zanga-zangar a sassa daban-daban kan tsadar rayuwa da ake fama da ita a ƙasar wadda ta gudana a tsakanin 1 da kuma 10 ga watan Agusta.
Tawagar Femi Falana tace hukuncin da ya bada damar tsare ƴan zanga-zangar na ƙunshe da danniya da rashin gabatar da hujjoji bisa tsari.
Ta kuma nemi kotun ta bada umarnin beli ƴan zanga-zangar zuwa ga ƴan sanda don su cigaba da walwala acikin al’umma.
