Shugaban hafsan sojojin Nijeriya Laftanar Janar Taoreed Lagbaja ya yi kira ga ƴan ƙasa nagari da su taimaka wajen ganin Nijeriya ta samo tsaro domin zaman lafiya.
Yayi wannan kiran ne a yayin rufe taron Hafsan Sojojin Nijeriya na tsakiya da ƙarshen shekara wanda a ka gudanar a babban birnin Jihar Akwa-Ibom, Uyo.
Lagbaja ya bayyana cewa rundunar soji na ƙoƙari sosai wajen ganin sun sami haɗaka mai ƙarfi da sauran hukumomin tsaro da ke ƙasar.
Taron ya ba kwamandojin yaƙi damar ganawa da junansu domin tattaunawa da kuma bada shawara domin ganin sun inganta yanayin ayyukansu a faɗin ƙasar.
