Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Majalisar dattawan Nijeriya ƙarƙashin mataimakin majalisar sanata Barau Jibrin, ya jagoranci ziyarar ta’aziya na mutuwar mahaifiyar tsohon shugaban ƙasa marigayi Malam Umaru Musa Yar’adua a Katsina.
Marigayiyar Hajiya Dada Musa Yar’adua ita ce kuma mahaifiya ga marigayi Shehu Musa Yar’adua da shugaban kwamitin harkokin soja a majalisar dattijai sanata Abdulaziz Musa Yar’adua.
Sanata Barau Jibrin ya yi addu’a Allah yafe mata kura kuran ta ya albarkaci abinda ta bari.
Ya kuma shawarci sanata Abdulaziz Musa Yar’adua da ya ɗauki mutuwar ta a matsayin sa na musulmi
da babu wanda zai wuce lokacin sa.
Ya bayyana Marigayiya Dada a matsayin mace mai taimakon al’umma inda a kullum akwai dandazon mabuƙata da take taimaka masu da maƙota suka shaida.
A cikin waɗanda suka rufa masa baya akwai sanata Abdulhamid Musa shugaban kwamitin harkokin ‘yan sanda da sanata Aminu Iya Abba mai kula da kwamitin kimiya da fasaha .
Akwai kuma sanata Muntari Ɗandutse mai wakiltar shiyar Funtua a jihar Katsina.
