
Daga BELLO A. BABAJI
Akwai manyan alamu da ke nuna cewa kamfanin man fetur na Ƙasa, NNPCL ya umarci rassansa su mayar da farashin litar mai zuwa Naira 855.
A ranar Talata ne aka ga gidajen man sun sauya farashin litar mai daga N600 zuwa N855 inda wasu ke cewa an samu umarnin ƙara farashin ne ga gidajen man.
Umarnin ya sanar da cewa hukumar gudanar da gidajen man ta yi kwaskwarima ne wa farashin mai a dukkan rassansa.
Haka na zuwa ne kwana biyu da kamfanin ya sanar da cewa ya na fuskantar matsaloli a yayin shigo da man fetur Nijeriya sakamakon bashin Dala biliyan 8 da ake bin sa.
Yayin da manema labarai suka nemi mai magana da yawun hukumar, Olufemi Soneye don ya yi magana a madadin shugaban kamfanin (GMD) Mele Kyari, ya ƙi amincewa da yin tsokaci akan hakan.
An kuma gano cewa wasu gidajen mai na ƴan kasuwa, sun sauya farashinsu zuwa N860 a yan kwanakin nan.
