Marigayiya Dada Yar’Adua uwa ce ga Nijeriya – Gwamna Raɗɗa

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

An bayyana Marigayiya Hajiya Dada Musa Yar’adua a matsayar uwa ba wai ga Jihar Katsina na kawai har ma Nijeriya baki ɗaya.

Hakan ya fito ne daga bakin Gwamna Dikko Raɗɗa na Jihar Katsina a hira da manema labarai a gidan sa da ke gidan gwamnati.

Ya ƙara da cewa Allah ya albarkace ta da ya’ya da suka riƙe shugabancin Nijeriya wanda haka bai sa ta canza mu’amullanta da al’umma ba.

Gwamnan ya bayyana cewa a koda yaushe cikin hidimar taimakawa mabuƙata ta ke kamar yadda duk mai wucewa kofar gidan ta ya gani.

” Allah ya albarkace ta da ya’ya kamar su marigayi Shehu Musa Yar’adua da ya riƙe muƙamin babban hafsan hafsoshi Nijeriya da marigayi Malam Umaru Musa Yar’adua da ya riƙe muƙamin shugaban ƙasa da sanata Abdulaziz Musa Yar’adua da yanzu sanata ne”Dikko Raɗɗa ya ce.

Ya cigaba da cewa wannan babban baiwa ce da Allah ya yi mata amma bata canza fuska ba wajen tausaya wa al’umma.

Gwamnan yayi fatan Allah karɓi shahadar ta, ya kai rahama ga kabarin ta.

Ya kuma miƙa godiyar sa da wakilin shugaban ƙasa kashim shetima da tsohon mataimakin shugaban ƙasar Atiku Abubakar da gwamnoni da ‘yan majilisar ƙasa da sauran manyan mutane da suka halarci jana’izar marigayiyar.

By ukarofi