
Daga BELLO A. BABAJI
A ƙoƙarinta na rage raɗaɗin ƙunci ga al’ummarta, Gwamnatin Tarayya ta bai wa kowacce jiha Naira biliyan 3 don a raba wa mutanen da ambaliyar ruwan sama ta rutsa da su a matsayin tallafi gare su.
An sanar da haka ne a ranar Laraba, yayin wani zama da Majalisar Tattali ta Ƙasa da aka yi a Fadar shugaban ƙasa da ke Abuja.
Zaman, wanda Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima ya jagoranta, ya samu halartar gwamnoni da mataimakan gwamnoni da ministocin Nijeriya.
Sannan, shugaban tsarin ‘Bills and Belinda Gates Foundation’, Bill Gates da kuma shugaban rukunin kamfanin Ɗangote, Alhaji Aliko Ɗangote sun gabatar da jawabi a taron.
A lokacin da ya ke ganawa da manema labarai, gwamnan jihar Bauchi, Bala Muhammad ya ce, wasu jihohi a Arewa sun samu mafi munin ambaliya da ta haifar da rasa rayuka da dukiyoyin al’umma.
Ya bayyana cewa, kuɗaɗen za a yi amfani da su ne wajen rage raɗaɗi ga waɗanda ambaliyar ta rutsa da su wajen ba su kayan abinci da sauran nau’ukan ababen tallafi musamman ga waɗanda suka rasa gidajensu.
Majalisar ta kuma umarci a gudanar da bincike kan matakan damejin da ambaliya ta yi dukkan sassan Nijeriya.
