Ina fatan taken wannan maƙala ta wannan mako za ta ba da ma’ana da wuri wajen fahimtar darasin da na ke son tabowa da ya shafi marigayi Sarkin Gobir Muhammad Isah Bawa. Marigayin dai kafin wannan lokaci na juyayi da Allah ya karɓi rayuwar sa ya na sarauta ne a Gatawa a sanadiyyar rage ma sa girman sarautar Gobir da ke Sabon Birni kakaf. Gabanin kama shi da fitowar faifan bidiyon nan da ya nuna shi cikin jini ya na tare da ’yan ta’adda, mutane da yawa ciki har da ni ban san shi ba ko ban taɓa samun labarin sa ba a iya abun da zan iya tunawa yanzu. Hakan ba ya na nufin mutane ba su san tarihin ƙasar Gobir ko masarautar Gobir ba.
Tarihin Bawa Jangwarzo, Yunfa ko Nafata da mu ka samu daga tarihin Shehu Mujaddadi ɗanfodio ya isa mu san da zaman ƙasar Gobir. Ba mamaki dai ya zama wasun mu su ɗauka a sabon zamani masarautar Sokoto ta haɗiye ta Gobir ko sunan Gobir ya sauya zuwa babbar masarautar Daular da mujaddadi ya kafa. In an ambato Sokoto abu na farko da zai fadowa mutum kan sarauta shi ne sarkin musulmi wato Sultan. In an faɗaɗa bayanai wajen tuno ƙanin mujaddadi wato Abdullahi na Gwandu zai fahimci masarautar sa na jihar Kebbi ne. Rahoton da ya bayyana mutuwar mai martaba Sarkin Gobir Alhaji Isha Bawa a hannun barayin daji ya girgiza jama’a.
Tun fitowar faifan bidiyon da ɓarayin su ka ɗauka inda su ka nuna Sarkin na cikin mawuyacin yanayi da buƙatar ɗauki, mutane su ka yi ta kiran hukumomi su ɗau matakan ceto basaraken.
Alhaji Bawa wanda ya ce ya shafe fiye da shekaru 40 ya na hidima a matsayin Sarki ya buƙaci a kawo ma sa tallafi don samun fito da shi daga hannun barayin waɗanda haƙiƙa a faifan bidiyon sun raunana Sarkin don da alamun jini ma ya zuba a jikin sa.
An fahimci marigayin ya je wani mitin ne a Sokoto inda lokacin da ya ke dawowa a ka samu akasin.
Cikin dangin Hausawa za mu lura Gobirawa na daga waɗanda ba sa ɓuya don wasun su ma akwai inkiyar wato Gobir ko wane ai Bagobiri ne. Wani abu ma da a ka ba ni labari shi ne a wasu ƙasashe ko garuruwa da a ke da Sarkin Hausawa duk da haka a kan samu Sarkin Gobirawa. Irin wannan ba zai rasa nasaba da tsohon tarihin Gobirawa ba da kuma masarautar su da a ka ambata a wajaje daban-daban a rubutaccen tarihi. Kazalika Gobirawa na da wata tsaga a fuskar su da a ke gane su da ita. Duk wannan na nuna Gobirawa fitattun mutane kuma ba sa buya kusan a duk inda su ka shiga. Idan ka gamu da Bagobiri ka shaida shi da cewa Bagobiri ne za ka ga ya ji daɗi kuma ya amince da amsa hakan ne daga Gobir ya ke. Na ji wani malami na cewa Gobirawa na da jarumtaka ko tsayin daka kan abun da su ka saka a gaba. Lamuran rayuwar yau kan ɗau hankali ne bisa faruwar wani dalili wa imma na alheri ko sharri. Kamar yadda wasu dangogin jama’a ke da abokan wasa haka su ma Gobirawa na da irin waɗannan abokan wasa da in an gamu za ka ga a na zolayar juna a na raha ko dariya a rabu a na farin ciki. Ba don sauyawar zamani ba za ka tarar ba wani bambanci da a ke gani tsakanin juna ko da gari ko shiyya akwai bambanci. Matuƙar mutum ya fito daga yankin arewa to ɗan uwa ne ga sauran ‘yan arewa. Wannan dangantaka ba ga arewacin Nijeriya ta tsaya ba har zuwa Jamhuriyar Nijar. Idan al’ummar Nijar su ka shigo yankin Nijeriya a kan dauka duk dangin juna ne ba batun Bazabarme, buzu da sauran su. Rayuwa mai matuƙar ban sha’awa. Amma mu tuna lokacin da a ka samu juyin mulkin sojan nan na Nijar ƙarƙashin Janar Abdulrahman Tchiani an so samun rashin fahimta tsakanin al’ummar Nijeriya ko ma arewacin Nijeriya da ‘yan uwan su na Nijar. Cikin ikon Allah daga bisani akasarin waɗanda ba su gane ba sun gane cewa zumunci na nan kuma musamman Allah ya kiyaye ba a samu ɗaukar matakin soja kan gwamnatin Nijar ba bisa ƙudurin ƙungiyar raya tattalin arziki ta Afurka ta yamma wato ECOWAS ko CEDEAO. Taron da a ka gudanar kwanan nan na Hausa a Jamhuriyar Nijar ya ƙara kawo haɗin kai da dawo da zumunci irin na tarihi. Wato shi ya sa a ke gudun tashin fitina da wasu ƙalilan kan tado ta amma in ta taso sai sharrin ta ya shafi waɗanda ba ruwan su da ita ko a ce waɗanda ba su da hannu na nesa ko kusa cikin kitsa fitinar. Mu duba yadda fitinar Boko Haram ta yi sanadiyyar mutuwar dubban mutane kuma har yau wutar ke ciki daga tasowar fitinar tun shekara ta 2009. Ga shi batun satar mutane a arewa maso yamma tun a na batun barayin shanu har ya kai ga rikicewar lamura a ka koma ɗaukar mutane a shige da su daji a ci zarafin su a kuma nemi maƙudan kuɗin fansa. Kauyuka da a baya in gari ya yi zafi sai mutum yadaure kayan sa ya koma ƙauye don noma ko ma ’yar karamar sana’a amma yau an wayi gari gara ma mutum ya makale a gefen birane duk wahala ko tsadar rayuwa. Wasu fa a ƙauyuka kan kwana ne ido biyu buɗe don wasun su ma kan kwana kan rassan bishiyoyi.
Marigayi Sarkin Gobir na Gatawa ya samu gata don a na ta yi ma sa addu’ar Allah ya sa ya samu shahada. Barayin da su ka sace shi kuwa a Kwanar Mahalba na shan addu’ar Allah ya yi maganin su. Wasu limaman masallatan Jumma’a a sassan arewa sun jagoranci sallar jana’iza “GA’IB” wato ga wanda ba ya wajen da a ka yi sallar ko ma ba a samu yi ma sa sallar ba. An yi ta zuba ruwan addu’o’in Allah ya yi rahama ga marigayin. Kafafen labaru sun cika da bayanai na halin da a ke ciki kan marigayin inda har na ga waɗanda ke kiran ba da diyya.
ɗan majalisar dokokin jihar Sokoto Aminu Boza ya nesanta kan sa da hannu a kisan gilla ga mai martaba Sarkin Gobir Aminu Boza.
Boza na amsa tambayar manema labaru ne kan zargin da a ka yi ma sa na ba da Naira miliyan 5 ga ’yan ta’adda don su yi kisan gilla ga Sarkin Alhaji Isah Bawa.
Wani faifan bidiyo da ke nuna ɗan marigayi Sarkin na Gobir da a ka sace shi tare da mahaifin na sa amma a ka saƙo shi, ya baiyana ji daga ’yan ta’addan cewa Aminu Boza ne ya ba su kuɗin don kashe Sarkin.
Boza ya aza alhakin zargin sa da ’yan ta’addan su ka yi da yadda ya dage wajen yaƙi da su kuma ya ce sam ba zai yi kasa a guiwa ba.
Da ta ke martani kan gamayyar ƙungiyoyin arewa CNG ta bukaci zurfafa bincike da ɗaukar matakan shawo kan matsalar.
Shugaban amintattu na ƙungiyar Nastura Ashir Sharif ya ce a guji shigar da siyasa a lamuran tsaro har dai a na son samun nasara “lokaci ya yi da shugabannin mu na siyasa su san cewar su daina sa siyasa a cikin komai na rayuwa”
ɗan majalisa Boza ya yi alwashin ba zai saurarawa ‘yan ta’adda ba ko hakan zai kai shi ga rasa rayuwar sa “ina ji a raina ƙarshen ta mutanen nan ne za su hallaka ni kuma ni na yarda in mutu ta wannan hanyar, Allah ya sa mu ci nasara a kai ƙarshen su Insha Allahu”
A na cigaba da muhawara kan lamarin na rasa ran Sarkin Gobir da hakan ya ƙara nuna yadda taɓarɓarewar tsaro ta ƙara ta’azzara a arewa.
Tsohon ɗan majalisar wakilai Gudaji Kazaure ya nuna mamakin yadda marigayi Sarkin Gobir Muhammad Isah Bawa ke tafiya a mota shi kaɗai hatta ma ranar da a ka sace shi.
Kazaure wanda ke nuna juyayin kisan gilla ga Basaraken, ya ce labaru sun nuna ranar da a ka sace marigayin ya na komawa gida ne daga taron da ya shiga birnin Sokoto inda kuma a motar sa ma dan sa ne kaɗai ke tuƙa shi kuma hakan ya sa a ka sace su tare.
A nan Gudaji na da ra’ayin a matsayin marigayin na babban Sarki ya dace aƙalla ya zama ya na tafiya da rakiyar dogarai ko ma ba jami’an tsaro.
Kazalika Kazaure ya nuna damuwa kan jinkirin da ya ke ganin an samu wajen kai kuɗin fansar.
Kammalawa;
Yanzu dai an sace talaka an sace sarki. Duk wata dabara da za a bi a samu sauƙin wannan fitina ya dace a bi. Duk wasu har yanzu na ganin bude wuta ne hanyar maganin ’yan ta’addan na daji; a gaskiya an buɗe wuta ko ma a na buɗewa. Wani lokacin ma ba wuta a ke buɗewa ba a kan yi amfani da wuƙa a yanka wanda ’yan sa kai ke zargi da ba da labari ga ɓarayin. Addu’a makamin Mumini.
