
Daga BELLO A. BABAJI
Ƙarin farashin man fetur a Nijeriya ya sanya wasu mutane yin zanga-zanga inda suka yi gangami acikin garin Ilorin, babban birnin jihar Kwara.
Masu adaidata sahu sun dakatar da ayyukansu inda suka yi cincirindo da tare manyan titunan birnin kan matsin rayuwa da al’umma ke fama da shi a ƙasar.
Ganin haka ya sa wasu da ba su samu abin hawa ba su ke yin tattaki don zuwa wajen gudanar da harkokinsu.
Wani rahoto daga jaridar ‘News Point Nigeria’ ya ce, ƴan sanda sun tarwatsa masu zanga-zangar da hayaƙi mai sanya ƙwalla da aka fi sani da borkonon tsohuwa.
