Daga USMAN KAROFI a Abuja
Ƙasar Burkina Faso ta ƙaddamar da sabon fasfo maras tambarin ECOWAS, wanda hakan yana nuni da cewa ƙasar ta tabbatar da ficewar ta daga ƙungiyar ta ECOWAS.
Idan ba mu manta ba, ƙasashen Nijar, Mali da Burkina Faso sun fice daga ƙungiyar ECOWAS ɗin bayan sanya musu takunkumi da ƙungiyar ta yi a dalilin juyin mulki da ya faru a ƙasashen.
Duk da cewa ƙungiyar ECOWAS dakatar da ƙasashen ta yi, ƙasashen uku sun bayyana su ficewa za su yi wanda canza fasfo da ƙasar Burkina Faso ta yi ya jaddada haka.
Shugaban haɗakar ƙasashen ta ECOWAS Bola Tinubu ya bayyana har yanzu suna bakin ƙoƙarin ganin sun shawo kan ƙasashen domin su dawo.
