Ƙungiyar ’yan fansho ta bayyana takaici kan kuɗaɗen da ake biyan su

Spread the love

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Ƙungiyar ’Yan Fansho ta ƙasa (NUP) ta bayyana takaicin yadda wasu gwamnonin jihohi ke biyan ma’aikatan fansho.

Ƙungiyar reshen Jihar Kaduna ce ta bayyana haka, inda ta ce a wasu jihohin akwai tsofaffin ma’aikatan da ake biya N500 kacal.

Sakataren ƙungiyar na Kaduna, Alhassan Musa ya bayyana takaici matuƙa kan yadda ake biyan ‘yan fanshon.

Ya ce, bai dace a riƙa barin rayuwar ma’aikatan da suka hidimtawa ƙasa a cikin wahala ta hanyar biyansu ƙalilan ɗin kuɗi ba.

Wasu daga cikin ‘yan fansho a jihohin da ke Kudancin ƙasar nan  musamman jihohi masu albarkatun man fetur sun fi kowa rashin samun fansho mai kyau.

ƙungiyar yan fansho ta kasa ce ta bayyana takaicin haka, inda ta ce bai dace a ce jihohin da ke samun arzikin mai na biyan mafi ƙarancin kuɗin fansho ba.

Sakataren ƙungiyar yan fansho na jihohin Arewacin ƙasar nan 19, Alhassan Musa ya bayyana cewa ana biyan wasu ‘yan fansho N3500.

Ya ce, wuraren da lamarin ke da dama dama su ne babban birnin tarayya Abuja da wasu jihohin Arewa inda ake iya biyan har N18,000 duk wata.

By ukarofi