Ƙungiyar Afenifere ta buƙaci Tinubu ya shawo kan matsalar tsadar rayuwa da rashin tsaro

Spread the love

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Ƙungiyar Yarbawa ta Afenifere ta yi kira ga Gwamnatin Tarayya da tashi tsaye don ceto Nijeriya da al’ummarta daga durƙushewa gaba ɗaya.

ƙungiyar ta bayyana damuwarta game da barnata da dukiyar ƙasar a yayin da rayuwar al’ummar Nijeriyar ke ƙara taɓarɓarewar tun bayan hawa mulkin gwamnatin shugaba Bola Tinubu.

A cikin wata sanarwa da mataimakin shugaban ƙungiyar Oladipo Olaitandan da mataimakin sakatare na ƙungiyar, Alade Rotimi John suka fitar sun ce halin da ake ciki ya jefa ƙasar cikin wani yanayi na tsaka mai wuya da ruɗani.

“Alummar Nijeriya na cikin damuwa matuƙa sakamakon wahalhalun da ake fama da su da yunwa da rashin tsaro da tsaddar rayuwa da rashin aikin yi da kuma hauhawar farashin kayayaki”, inji ƙungiyar ta Afenifere.

Ƙungiyar ta ce waɗannan matsaloli sun ƙara ta’azara halin da alummar ƙasar ke ciki idan aka kwantata da na baya.

Ta nuna damuwa kan irin riƙon sakainar kashi da halin ko in kula da rashin hagen nesa da gwamnati Tinubu ke yi dangane da irin illar da ke tattare da manufofin gwamnati.

Game da haka ne ƙungiyar ta Afenifere ta yi gargaɗi kan ɓarnatar dukiyar ƙasa tana mai cewa, “Dala miliyan 300 kwatankwacin naira biliyan 240 da aka cire na sayan jirgin shugaban ƙasa da kuma karin naira miliyan 150 alamari ne da ba za a amince da shi ba’’.

ƙungiyar ta Afenire ta ce naira miliyan 950 kan sayan sabbin mottocin sulke samfurin Cardilac da limousine da kuma SUɓ a matsayin motocci na musaman ga shuagaban ƙasa da naira biliyan 21 don yi wa sabon gidan mataimakin shugaban ƙasa kwaskwarima da kuma naira biliyan 90 a matsayin tallafin kuɗin aikin addini na sauke farali da kuma naira biliyan 10 don yi wa gidan shugaban ƙasa a Lages kwaskwarima sun bayyana yadda ake almabaranci da dukiyar ƙasar.

“Abin kunya na ci gaba da rufeta game da rashin kimar ƙasar a idanun ƙasashen duniya kan yadda shugabanni ke karkatar da tunanin alummar ƙasar domin yin watanda tare da ɓarnata da kuɗin Nijeriya amma su ke nuna halin ko in kula game da illar abinda zai iya biyo baya”, inji Afenifere

ƙungiyar ta yi zargin cewa akwai rashin sanin ya kamata kan yadda ake barin talakawan ƙasar cikin kunci da kuma matsalolin tafiyar da alumaran mulkin ƙasar ba tare da bin ƙa’ida ba.

By ukarofi