An kama ɗan shekara 60 kan satar wayar lantarki a Katsina

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Rundunar tsaro ta al’umma (Civil Defence), ta yi nasarar kama tsoho ɗan shekara 60 kan satar wayar wutar lantarki a ƙaramar hukumar Funtua da ke jihar Katsina.

Jami’in yaɗa labarai na rundunar, DSC Buhari Hamisu ya bayyana sunan ɓarawon mai sun Hassan Abubakar da ke zaune a ƙauyen Lasanawa a garin Maska da ke ƙaramar hukumar.

DSC Buhari ya ce, Hassan ya zo hannun jami’an tsaro ne bayan an kama shi da tsinkakkun wayoyin lantarki ya na ƙoƙarin kai wa masu cinikin kayan nauyi a garin Funtua.

“Cikin dare ya hau sandar wayar wutar lantarkin da ke kan babban titin Lasanawa inda ya tsinke wayar ya sanya a buhu da ƙoƙarin kai wa masu cinikin kayan nauyi a garin Funtua, kana jami’an suka rutsa da shi mai laifin”, inji DSC Buhari.

Jami’in yaɗa labaran ya ƙara da cewa, wanda ake zargin ya amsa laifinsa kuma yanzu haka ya na tsare a hedikwatarsu inda da zarar sun gama bincike za su gabatar da shi a kotu.

Kwamandan hukumar tsaron na jihar, Jamilu Indabawa ya yaba wa jami’ansa bisa namijin ƙoƙarin da suke yi wajen daƙile aikace-aikacen ɓata-gari a faɗin jihar.

Haka kuma, Indabawa ya yaba wa al’ummar jihar wajen goyon baya da suke bai wa hukumar wajen yaƙar ɓata-gari musamman masu sace wayar wutar lantarki a manyan titunan jihar.

By Babaji