Gwamna Dauda ya ƙaddamar da asibitin Maru da aka gyara

Spread the love

A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan Sulaiman Bala Idris ya sanya wa hannu, ya tabbatar da gyaran asibitin Maru wanda mai girma Gwamna ya ƙaddamar a Asabar da ta gudana.

Sanarwar ta bayyana cewa, ba asibitin Maru kaɗai ba, duk sauran asibitoci da ke faɗin jihar su na nan ana aikin gyaran su.

Gwamnan a yayin ziyarar ya bayyana cewa kiwon lafiya na ɗaya daga cikin batutuwa da gwamnatin sa ta maida hankali a kai.

Wannan gyaran ya mayar da asibitin Maru na zamani da mutane za su ji daɗin zuwa domin duba lafiyar su da ma waɗanda ke maƙotaka da Maru. Domin gyaran ya sanya asibitin za iya gudanar da ayyuka da dama ciki har da yin tiyata.

Asibitin zai daina fama da rashin wuta domin an sanya solar mai kilowat 39 don ganin aiki bai tsaya ba saboda rashin wutar lantarki.

Daga ƙarshe ya gwaman ya umarci ma’aikatar lafiya da ta cigaba da aiki tuƙuru domin ganin yan ƙaramar hukumar Maru sun mori wannan asibitin yadda ya dace.

By ukarofi