
Daga BELLO A. BABAJI
Mataimakin shugaban Majalisar Dattijai, Sanata Barau Jibrin, ya ce Shugaba Tinubu bai gamsu da yadda aka bi ba a baya wajen rabon kayan tallafin ga mabuƙata a Nijeriya don rage raɗaɗin halin matsi da al’umma suka tsinci kansu a ƙasar.
Ya ce, kasancewar haka ne ya sanya shugaban yanke shawarar samar da kwamitin kula da raba kayan tallafin don a tabbatar da cewa ya kai mabuƙatan.
A lokacin da ya ke ƙaddamar da buɗe aikin raba tallafin gwamnatin tarayya na shiyyar Arewa-maso-Yamma a Kano ran Lahadi, Barau ya yi kira ga al’ummar Nijeriya su bai wa Shugaba Tinubu goyon baya wajen ganin an daidaita taɓarɓarewar lamuran ƙasar, ya na mai cewa yanzu ba lokaci ba ne na ɗora laifi.
Ya kuma ce, Shugaba Tinubu na aiki tuƙuru ta hanyar samar da tsare-tsaren farfaɗo da tattali don hakan ya kasance riba ga al’umma.
Tun da farko, Ministan Noma, Abubakar Kyari ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ta aika da tirela 90 na kayan abinci da kuma ƙarin wasu 20 don a raba wa al’ummar Kano waɗanda ba a raba su ba bisa tsari.
