
Daga BELLO A. BABAJI
Jami’an tsaro na hukumar ƴan sandan farin kaya ta DSS sun kama shugaban Ƙungiyar Ƙwadago ta Ƙasa, Joe Ajaero akan hanyarsa ta tafiya Burtaniya a ranar Litinin.
Jaridar ‘WikkiTimes’ ta ruwaito cewa, jami’an sun kama shi ne a lokacin da ya nufi ficewa daga Nijeriya don halartar taron Ƙungiyar Kasuwanci (TUC) a filin jiragen sama na Nnamdi Azikwe da ke Abuja.
A kwanakin baya ne rundunar ƴan sanda ta gayyaci Ajaero kan laifukan da ke da alaƙa da zanga-zangar tsadar rayuwa da aka yi a watan Agusta, inda gwamnatin tarayya ta zarge shi da hannu a laifukan da suka shafi cin amanar ƙasa.
