APC ta ɗage taron ta na masu ruwa da tsaki har illa masha Allah

Spread the love

Jam’iyyar APC ta ɗage taron ta na masu ruwa da tsaki da za a gudanar 11 da 12 ga Satumba har illa masha Allah.

Jam’iyyar ta bayyana cewa za ta sanar da sabbin ranaku da taron zai gudana.

Har yanzu jam’iyyar ba ta bayar da wani dalili na ɗage taron ba, amma bayanai da jaridar Blueprint Manhaja ta samu shine, rashin shugaban ƙasa yana ɗaya daga cikin dalilan ɗage taron.

Kuma takardar sanarwa wadda jami’in hulɗa da jama’a na jam’iyyar Felix Morka ya sanyawa hannu ta yi kira da cewa duk masu ruwa da tsaki su lura da wannan sanarwa sannan sabbin ranakun taron za a sanar nan ba da jimawa ba.

By ukarofi