Daga NASIR S. GWANGWAZO
“Hanyar Cigaban Arewacin Najeriya!”
A wani yunƙuri na inganta kula da kiwon lafiya, asibitin ƙwararru na Best Choice ya ɗauki gabaren kula da kiwon lafiyar jarirai tare da ƙaddamar da Sashin fasaha don kula da Lafiyar Jarirai da aka tsara don magance ciwon shawara da hana lalacewar kwakwalwar ga jarirai.
A cikin wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun shugaban asibitin, Auwal Muhammad Lawal, ya lura cewa na’urar ita ce irinta ta farko, wanda ƙwararrun likitoci ke amfani da ita wajen juyen jini cikin fasaha don inganta sakamakon jiyya ga yara.
A nan ɓangaren Dr Abdulmalik Saminu ya bayyana cewa, na’ura ce mai cike da fasaha dake ɗaukar nauyin fitowar haske kaso 70% na ban mamaki da ke daidaita buƙatar ƙari ko juyen jini.
Ya ƙara da cewa, ɓullo da wannan na’ura ta zamani ya nuna wani gagarumin ci gaba ne da Asibitin Best Choice ya bullo da shi don kula da kiwon lafiyar jarirai.
Saminu ya ce, sashin Kula da Lafiyar Jarirai na iya yin maganin ciwon shawara yadda ya kamata cikin ƙwarewa ba tare da daukan yin doguwar jinya ga iyalai ba da kuma saukin kashe kuɗaɗe.
“Mun fahimci irin yadda iyaye ke faman shan wahala game da yanayin lafiyar ƙananan yara.
“Saboda haka ne muka mai da hankali kan wannan fasaha don sauƙaƙe nauyin da ke kan iyalai da kuma samar wa yara yanayi mafi kyawu, domin samun rayuwa mai kyau,” inji Auwal.
Shugaban asibitin ya bayyana cewa na’urar ita ce irin ta ta farko a Arewacin Nijeriya, kuma ta uku a faɗin Najeriya, kuma tana ba da cikakkiyar kariya da maganin jiyya ga jarirai.
Dr. Abdulmalik Saminu, babban ƙwararre likita ne a fannin kiwon lafiya ya bayyana fatansa cewa wannan ci gaban zai kara karfafa matsayin asibitin Best Choice a matsayin jagora a fannin kula da kiwon lafiyar ƙananan yara, tare da baiwa iyalai ƙwarin gwiwa kan kula da ‘yan uwansu.
Saminu daga nan ya godewa mamallakin asibitin bisa namijin ƙoƙarin da yayi na samar da wannan wannan fasaha ta zamani duk da bala’in tsadarta.
Da wannan sashen Kula da Lafiyar Jarirai ne, iyalai da ‘yan uwa ba sa buƙatar neman tafiya ƙasashen waje don neman magani, kamar yadda asibitin Best Choice, wanda ke kan titin Aminu Kano kusa da Tal’udu a birnin Kano, ke bayar da kulawa ta musamman a cikin gida.
