(Ci gaba daga makon jiya)
Daga MUKHTAR YAKUBU
A satin da ya gabata, mun faro tattaunawa da fasihin marubuci da ya jima yana yi wa adabi hidima. Marubucin da ya fara rubuta littafin fasahar sadarwar cikin harshen Hausa.
A tattaunawar makon jiya, ya yi mana bayanai da dama, tun daga yadda ya fara, har zuwa yadda ya zama cikakken marubuci, da kuma irin gudunmawar da ya bayar.
A wannan makon, da yardar mai dukka, za mu fara da tambayar da muka kwana kanta, kafin wasu tambayoyin su biyo ba.
MANHAJA: Ya kake ganin yadda matasan mu za su ci gajiyar ilimin fasahar sadarwar da bayanai a wannan lokacin?
ABUBAKAR TSANGARWA: To a gaskiya a yanzu ita duniyar ta zama kashi biyu, akwai masu duniyar a hannun su akwai kuma waɗanda muke ganin kawai kamar an ɗauke mu ‘yan rakiya ne. To irin waɗannan matasan namu, duk inda ka shiga, za ka yi magana a kan abu biyu ne. Waɗannan dai wake- waken kade -kade da raye-raye su ne abin da suka fi so da kuma mayar da hankalinsu a kai. Don a wasu ƙasashen ma har gara namu matasan, saboda za ka ga ai mu namu suna ƙoƙarin koyon sana’ar kwamfiyutar kamar abin da ya shafi tura waƙa da kuma gyaran kwamfiyuta ɗin da zane-zane.
Wannan matasanmu suna yi sosai, kuma wannan harkar ta Cripto ma idan ka zo, kai ka ce a Kano aka ƙirkire ta. To ka ga muna ƙoƙari kenan a kan abin da ya shafi fannin kwamfiyuta. Saboda matasan mu na Afirika an riga an kashe musu gwiwa an koya musu son nuna isa, kuma babu isar. Wanda wannan abin yana ba ni mamaki sosai, za ka ga matashi aljihun sa babu komai amma so yake ya yi tafiya yana takama, da kuma takama cikin magama, don haka matasa su gane, ita tafiyar takama da saka rigaga magana duk isa ce da sai mutum ya isa yake yi.
Wanne ƙalubale ka samu a cikin wannan harkar?
To ni ka ga kamar yadda nake faɗa a kowacce lokaci. ƙalubale a cikin komai alama ce ta yin nasara. Duk abin da za ka yi fafutuka a ciki aka ce babu ƙalubale, to kaima ka tambayi kanka. Amma Allah ya kan yi misali. Tun da a al’adance an san cewa duk abin da za a yi nasara ana shan wahala. To waɗansu kuma ya kan zaɓe su ya ba su ba tare da wahala ba, to wannan shi ne ake kira baiwa. Don haka bakin gwargwado, a iya tsawon shekaru da aka yi ana yin wannan fafutuka, mun ga abubuwa iri iri bakin gwargwado, ko kuma ana ma kan gani. Wani idan ya zo, shi burin sa kawai ya mayar da kai saniyar tatsa, shi ba shi da wata buƙata ta da wuce wannan, ba wai so yake ya cutar da rayuwarka ba, a’a, so yake ka zamar masa saniyar tatsa ta yadda ba ka da katabus, shi zai je ya karɓo aiki ya ba ka ka yi, ya ɗan sammaka abin da yake so. Akwai waɗanda su so suke ma su je su boye ka a ɗaki ma kar a ji ɗuriyar ka, ta yadda duk abin da ka yi a ce su suke yi. Kuma da zarar ka ce ba za ka yi ba, farkon abin da za su fara yi, shi ne su yake ka. Sannan kuma a sama da wannan, babu abin da Allah bai yi mana ba na rufin asiri, don kamar yadda ka faɗa, ni babu wani abu da nake yi in ban da kwamfiyuta, don ko rubutu da nake yi sai na yi amfani da ita. Saboda haka bakin gwargwado ta haɗa mu da mutanen arziki. Kuma bakin gwargwado ana iya ɗan samun abin da ake gudanar da rayuwa da shi, wanda kuma wannan shi ne babban abin da ake buri. Sauran abin da Allah ya ajiye a gaba kuma bamu sani ba. Kuma babban abin da ya fi damu na tsawon lokaci shi ne, ya za a yi rayuwar mutum ta zama ta amfanar da al’umma. Shi ne abin da ya fi komai muhimmanci. Idan ina da sha’awa ta irin waɗannan abubuwan da ake yi na hawa manyan motoci, to gaskiyar magana da tuni an daɗe a wannan wajen. Amma buƙatar ta nake da ita shi ne, ta ya zan samu abu ta hanyar halal wanda gumi na ne ya ba ni. Kuma ya za a yi rayuwata ta amfanar da al’umma, wannan shi ne. Idan mutum ya zo, kuma na ga ra’ayin mu bai yi daidai da shi ba, sai ya kama gaban sa na kama gaba na. Amma ita mugunta ta a toshe maka wasu abubuwan, idan ka ga ba a yi maka, to ba ka da mamora. Dole ka na fitowa, wani ba zai tsaya ya fahimce ka ba, sai ya ce za ka zama barazana a gare shi.
Akwai wanda ma babba ne, da zan ambaci sunan sa za ka yi mamaki. Wallahi ina ji yake cewa “Wannan fa sai mun yi da gaske.” Kuma sun yi ita da gasken nasu, kuma Allah ya tsallakar da mu. Tun daga nan da suka koma gefe suka yi shiru da bakin su ba su ƙara cewa komai ba. Kuma wannan Allah ne yake yi ba mu ba. Don haka kowanne ɓangaren an samu daidai gwargwado na abin da za a samu, ta ɓangaren jarrabawa an gani ko ana gani. Ta ɓangaren samun damarmaki na rayuwa ana samu an gani. To duk abin da za ka iya tunani wanda mutum yake fata shi ne Allah ya haɗa ka da jama’a ta arziki da mutane na arziki, kuma akwai su. Don akwai waɗanda da sun ji an ce wane, ba wai sai sun jira wane ya zo ya yi ƙorafi ba, a’a, daga sun ji an ce damuwa ce ta wane. To za ka ga sun yi iya bakin ƙoƙarin su na su ga cewar sun magance wannan matsalar, akwai su. Akwai waɗanda da idan suka gan mu, tsakanin mu da su a shekaru da karatu da tattalin arziki da sarautar nisan ya yi yawa, amma kuma ka ga sun zo sun jinjina maka. To ka ga babu abin da ya kai wannan daɗi, ya zama duk wajen da ka je ana mutunta ka, don haka za mu iya cewa Alhamdulillah bakin gwargwado.
Wanne kira za ka yi ga matasa a game da wannan ilimi na fasahar sadarwar da bayanai?
To ni kiran da zan yi ga matasa shi ne dai ko da wanne lokaci abin da mutum ya yi imani da shi, to shi yake kiran mutane, ba a kan abin da bai gamsu da shi ba. Duk irin waɗannan soki burutsu da zage zage da matasa suke yi a Soshiyal Midiya ba ta burge ni, ina ganin babban abin da ya kamata matasan mu su mayar da hankali a kai, shi ne ya za a yi na taimaki kaina. Ba wai sai wane da wane ba. Shi kansa wanen nan, yadda aka haife ka haka aka haife shi. To me ya sa kai ba za ka yi tunanin wacce hanya za ka bi ka taimaki kanka ba. Kuma hanyoyin taimako kamar yadda na ke faɗa suna da yawa. Idan shekaru sun kai, to rayuwa mataki mataki ce. Idan an wuce lokacin karatu kuma ba a cikin sa ake ba.
Sai a gwada kasuwanci. Shi ma idan aka ga ba zai yiwu ba, akwai noma, idan shi ma ba zai yiwu ba, akwai sana’ar hannu. Kuma kowanne da na faɗa maka ɗin nan ya na da faɗi da yawa. Don haka babbar shewara ta ga matasa, ita ce, a rungumi harkar karatu ta harkar ilimin fasahar sadarwar da bayanai, domin ita ce matuƙar dai ka iya, to za ka samu aiki, babu wani batun hanya ko gata a ciki. Saboda harkar sadarwa ake so a yi, kuma ɗan gatan bai iya ba, wanda shi iya gatan da za a yi masa shi ne a ba shi kuɗi miliyan goma, shi kuma dole sai ya je ya nemo wanda yake da ilimin fasahar sadarwar, to idan ka iya, kada ka damu da miliyan gomar sa, ya ɗauki miliyan tara ya ba ka miliyan ɗaya ka yi masa, ka je ka ci abinci kawai, su je can su karata da waɗanda suka ci amana da kuma tsakanin su da Allah, kai dai abin da ka sani, ka yi aiki an biya ka gumin ka. Ina da tabbas duk wanda ya riƙe wannan, to gaskiyar magana da wahala ya shiga hali na babu, da fatan matasa za su yi abin da ya dace.
To Madalla mun gode.
Ni ma nagode sosai da damar da aka ba ni.

