
Daga BELLO A. BABAJI
Shugaban Ma’aikatan Tsaro (CDS), Janar Christopher Musa ya tabbatar wa al’ummar Nijeriya cewa nan ba da jimawa ba za su kama shahararre kuma shugaban ƴan ta’addar nan, Bello Turji.
Janar Musa, ya faɗi haka ne a ranar Talata, a lokacin da ya ke ganawa da manema labarai a Abuja yayin bada bayanai game da ayyukan jami’an tsaro a Nijeriya.
Ya ce, “kama Turji na daf da faruwa”, inda ya bayyana ɗan ta’addan a matsayin wanda ke jin ya bunƙasa, ya na mai cewa hakan na wani ɗan lokacin ne yayin da jami’an sojoji ke cigaba da farautar sa.
Janar Musa ya yi iƙirarin cewa, “za mu kai gare shi, sannan ina tabbatar muku cewa nan ba da jimawa ba za a warware wannan matsalar.”
Ya yi kira ga al’umma da su bada haɗin-kai wa jami’an tsaro ta yadda za su ke kai duk wani bayani da ya shafi zirga-zirgar ƴan ta’adda, ya na mai roƙon su da kar su bai wa ƴan bindigar kowacce irin taimako.
Bugu da ƙari, duk waɗannan ƙalubale, ya tabbatar wa al’ummar Nijeriya cewa jami’an soji da haɗin-gwiwar sauran hukumomin tsaro na cigaba da aiki tuƙuru wajen ganin an kawo ƙarshen rashin tsaro da kuma dawo da zaman lafiya mai ɗorewa a ƙasar.
Kazalika, ya yi kira ga gidajen jaridu da al’umma baki ɗaya su taimaka wa sojoji a ƙoƙarinsu na bai wa ƙasar tsaro.
