Daga ZUBAIRU LAWAL a Lafiya
Kungiyar da ke fafutukar haɗa kan ’yan Nijeriya ta ‘Advocacy for Integrity and Rule of law Initiatiɓe’ (AIRLIN) ta gudanar da taron wayar da kai ga ƙungiyar makafi masu fama da lalurar rashin gani a gidan makafi da ke garin Lafia, babban birnin Jihar Nasarawa a ranar Asabar.
Taron ya samu halartan Sarkin Makafi. Jihar Nasarawa Alhaji Bala Danladi da Sarkin Makafin Jos Alhaji Aliyu Muhammad Dahiru da sauransu.
Tawagar ƙungiyar ƙarƙashin Jagorancin Kodinetan na Jihar Nasarawa Alhaji Ibrahim Lawal Ibrahim da Kodinetan na ƙaramar Hukumar Lafia da na ƙaramar hukumar Awe da membobin ƙungiyar.
Cikin jawabinsa Shugaban ƙungiyar Alhaji Ibrahim Lawal Ibrahim ya ce; haƙƙin wannan ƙungiyar ce ta zagaya ko ina ta wayar da kan al’umman Nijeriya yadda za su kuɓutar da kansu daga halin da ake ciki.
Ya ƙara da cewa, ’yan Nijeriya suna zaɓe mutani a lokacin zaɓe amma mutanin ba su tsinana masu komai, da zarar sun hau mulki.
Ya ce, daga yanzu duk ɗan siyasan da ya zo niman ƙuri’arku ku nuna masa buƙatunku ga matsalar gidanku ya fara yi ma ku kafin Ku zaɓe shi.
Ya ci gaba da cewa, idan ya ce sai ya ci zaɓe zai gyara maku gidanku to ku gaya masa adadin ƙuri’unku kuma ba za ku bashi ba. Domin ba zai tsinana maku ko mai ba, ƙuri’anku yake buƙata.
Ya ce, yanzu aikin gwamnati ya yi wahala sai da kuɗi ake ba mutum aiki. Idan sunzo yi ma ku kamfen ku gaya masu ga yaranku su neman masu aiki kafin lokacin zaɓe idan suna buƙatar ƙuri’anku.
Kodinetan na jihar Nasarawa Alhaji Ibrahim Lawal Ibrahim ya yi kira ga Makafi da su tura yaransu zuwa makaranta domin samun ilimi mai inganci saboda cigaban rayuwarsu.
Ya ce, ba lallaine yadda kuke bara ace yaranku suna yawon bara ba. Domin da dama yaranku Allah bai yi su da lalurar makanta ba. Yayisu da idanunsu biyu biyu suna gani don haka suna da rawar da za su taka wajen cigaban kasan nan idan suka samu ilumi.
Ya ce; duk cikanku babu wanda baya son ace don shi ya zamo kwamishina ko gwamna ko shugaban ƙaramar hukumar.
Ya ce, duk na Allah ne amma sai da ilimi domin Allah yace tashi in taimake ka.
Daga ƙarshe, ya yi kira gare su da su yi katin zaɓe saboda niman ’yancinsu na zaɓen shugabannin da za su yi masu adalci.
Ya kuma buƙace su da su yi katin ɗan ƙasa saboda yana da muhimmanci. Ya ce, gwamnati tana ba da tallafi, wani lokacin akan buƙaci lambar katin ɗan ƙasa idan baku da shi wannan tallafin kun rasa shi.
Shima a nasa jawabin, Sarkin Makafi na garin Jos Alhaji Aliyu Muhammad Dahiru ya ce; haƙiƙa abinda Shugaban ƙungiyar ya faɗi gaskiyane. Ya kuma taɓo masu inda yake masu ƙaiƙayi.
Ya ƙara da cewa, lallai za su tanadi katin zaɓe maza da mata manya da yara. Da shi za su ƙwato ’yancinsu.
Yace: Sau da yawa mutane suna zuwa lokacin zaɓe su nemi ƙuri’unsu, su kuma yimasu alƙawari amma da zarar sun ci zaɓe baka ƙara ganinsu.
Shima Sarkin Makafin jihar Nasarawa Alhaji Bala Danladi ya yi godiya ga wannan ƙungiyar ta AIRLIN inda yace; bai taɓa ganin ƙungiyar da ke kishin ’yan Nijeriya ba kamar wannan.
Ya ce, duk manufofin da suka faɗi mai kyau ne, kuma da al’umman Nijeriya za su yi amfani da shi da an samu haɗin kai da shugabannin na gari.
Ya ce, wannan shawarar za su amfani da shi kuma suna goyon bayan wannan ƙungiyar ɗari bisa ɗari.
Shi ma Wakilin Makafin Lafia Malam Haladu Muhammad ya yi godiya da nuna jin daɗi.
Ya ce, rashin mallakar katin zaɓe da sauransu yasa gwamnati take mantuwa da su cikin tsarinta.
Ya ce, ko tallafine Gwamnati za ta raba baya ƙarasowa garesu. Yace wani lokacin ƙoƙari ake yi a hanasu barar da suke yi a ce suna damun jama’a.
Tunda farko cikin gabatarwarsa Alhaji Lawal Zubairu Muhammad ya bayyana manufofin wannan ƙungiyar.
Ya ce; ƙungiya ce ta duk wani mai buƙatar ganin an daura Nijeriya kan turba na gari ta yadda za a samar da kyakyawar shugabanci.
Ya ce; dole sai an samu dai daito da haɗin kai, inda ya ce ƙungiyar tana wayar da kan matasa illar shaye-shaye.
Sannan ƙungiyar tana wayar da direbobi illar tuƙin ganganci da ke janyo asarar rayuka da ɓarnar dukiya.
Ya ce, ƙungiyar tana da rassa a jihohi da dama a Arewacin Nijeriya kuma babban ofishinta na Abuja.
