
Daga BELLO A. BABAJI
Ƙungiyar Ƙwadago ta Ƙasa, NLC ta yi watsi da rahotannin da ke cewa hukumar ƴan sandan farin kaya ta DSS sai da ta gayyaci shugabanta, Joe Ajaero kafin ta kama shi kasancewar bai amsa ba.
Ta bayyana hakan a matsayin ƙarya da kuma salon ruɗar al’umma, ta na mai cewa Ajaero na da tarihin amsa gayyata daga hukumomi.
A kwanakin baya ne aka kama Ajaero a Filin jiragen sama na Nnamdi Azikwe da ke Abuja akan hanyarsa ta zuwa Burtaniya don halartar taron Ƙungiyar Kasuwanci ta TUC.
Yayin da DSS ta ke samun suka game da batun, sai ofishin shugaban ƙasa ya ce babu wanda ya fi ƙarfin doka kuma ma da Ajaero ya bai wa hukumar haɗin-kai game da buƙatarta.
A lokacin da ya ke kare zargin, jami’in hulɗa da jama’a na ƙungiyar, Benson Upah cikin wata takarda da ya fitar, ya musanta kiranye da DSS ta ce ta yi wa Ajaero, ya na mai cewa kafin a kama shi, sai da suka yi wani zama da Darakta-Janar na DSS a yayin wani ziyarar girmamawa wanda daga baya suka shirya sake zaman da nufin za a sanar da ranar haɗuwa acikin kwanaki biyu.
Takardar ta ce, sai da Ajaero ya bayyana shirinsa na tafiya halartar taron ga Daraktan na DSS inda ya ce masa zai kawo ziyarar bayan ya dawo daga tafiyar.
Baya ga haka ne a yayin ficerwarsa daga Nijeriya, jami’an DSS suka kama shi kan cewa ya na daga cikin waɗanda aka sanya sunayensu a jadawalin waɗanda ake nema a madadin wata hukuma.
NLC ta ce, Ajaero ɗan ƙasa ne mai mutunta doka da ke jagorantar ƙungiya mai kishi da ke da mutunci a idon duniya.
